Yayin da ake tinkarar batutuwan yanke hulda da sake kafawa a tsarin samar da kayayyaki na duniya, kasar Sin ta gabatar da sabon tsarin samun ci gaba, wato daga samar da takalma miliyan 100 zuwa kera mattarar bayanai ta microchip ga duniya, lamarin da ya sa kaimi ga yin amfani da katafariyar kasuwar cikin gida wajen raya fasahohin zamani.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi hangen nesa a kan cewa, ya kamata a raya kasar da kanta, da raya kasuwar cikin gida, ta yadda za a iya kiyaye samun ci gaba bisa yanayi mai canjawa sosai a duniya. Yayin da ake kokarin tabbatar da bunkasar tattalin arziki, kasar Sin ta yi amfani da kirkire-kirkire don tinkarar yanayin, wanda Amurka take hana bunkasar fasahohin zamani ta kasar Sin.
- Binciken Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Ya Nuna Gazawar Gwamnatin Trump Kwanaki 100 Bayan Kama Aiki
- Binciken Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Cin Zali Ta Hanyar Kakaba Haraji Ya Illata Kimar Amurka
Raya sabon tsarin samun ci gaba, ba ya kunshi raya kasa ko cikin gida ne kawai ba, ya kamata a kara bude kofa ga kasashen waje, da sa kaimi ga kasa da kasa don su more damammakin kasuwar kasar Sin da kirkire-kirkire da hadin gwiwa tare da kasar Sin.
Kamar yadda firaministan kasar Malaysia Anwar bin Ibrahim ya fada a kwanan baya cewa, yayin da kasa da kasa ke fuskantar mawuyacin hali, suna bukatar samun tabbaci da wani nagartaccen shiri na samun ci gaba. Don haka, ana ganin yadda kasar Sin ta samu nasarori, an nuna yabo ga kasar ta Sin, kasar Sin ta kawo tabbaci da kuma kyakkyawar makoma ga duniya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp