Assalamu alaikum masu karatu, barkan mu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Ado Da Kwalliya. Yau kuma za mu yi magana kan yadda ake hada sabulu na musamman domin gyaran fata da hadin Dilka:
Abubuwan da uwargida za ta tanada domin kyawun fuska:
Garin zogale, farar albasa, sabulun Ghana, sabulun Dettol, sabulun salo:
Yadda za ki hada:
Ki samu sabulun Ghana da na salo dai dai kai daya, sai ki samu Dettol shima kamar guda 2, sannan sai ki sami garin zogale cokali 2 sai albasa manya guda 2, duk sai ki hada su a turmi ki kirbe su, sannan sai ki juye a roba mai murfi za ki dunga wanke fuskarki da shi yana da kyau sosai yana magance kurajen fuska.
Hadin Dilka:
Abubuwan da za ki tanada:
Dilka da sukari, lemon tsami, man zogale, Turaren Du’aul Jannah
Yadda za ki hada:
Za ki zuba duk kayan a cikin ruwa sai ki sa wuta amma kadan har sai ya tafasa ya yi kumfa, sai ki sauke idan ya huce ki rinka dangwala kina shafawa a ko ina a jikinki, ki bari ya bushe, zai fara murmushewa da kansa sai ki karasa murje shi sai ki yi wanka da ruwan dumi, fatarki za ta yi kyau
Hadin sabulu na musamman:
Kayan hadi:
Madarar turare, Lalle Da Dilka, Ganyen Magarya, Kurkur, Dudu Osun Da Detol, Sabulun Ghana:
Yadda za ki hada:
A hada su wuri daya a daka su a turmi mai kyau su hade jiknsu sosai sai ki rinka wanka da shi. Sabulun wanka na Ghana:
Kayan hadi:
Kur-kur, Dilka, Zuma Kwai, Lemon Tsami.
Yadda zaki hada: Za ki hade su a guri guda ki samu ruwan ki kwaba kamar yadda ake kwaba lalle, amma ya fi kwabin lallen ruwa, sai ki shafe fuskanki, idan kuma har da jiki kike so, sai ki shafa har da jikin bayan awa daya sai ki shiga wanka za ki ga yadda jikinki zai goge tas da izinin Allah. Domin wannna hadin shi ake kira Dalleliya.
Ga kuma wani hadin, shima na gyaran fatan jiki zaki tanadi:
Lalle, Kwaiduwar Kwai 3, Manja Cokali 3, Kur-Kur.
Sai ki kwaba su guri guda ki shafe jikinki zuwa awa guda, sai ki yi wanka da ruwa zalla sai ki jika duka da ruwan dumi ku shafe jikin da ita sai ku kuma yin wanka.
Allah ya taimaka.
Za mu ci gaba daga mako mai zuwa in Allah ya kai mu.