Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da ajandar mulkin duniya a taron “SCO+” na birnin Tianjin a jiya Litinin. Wannan ajanda, ta nuna hanyar da za a bi, tare da ba da jagoranci ga aiwatar da ayyukan gina tsarin mulkin duniya mai adalci da dacewa, a karkashin yanayin duniya mai fuskantar manyan sauye-sauye, da kuma jagorancin cike gibin kudi na samar da ci gaba da bunkasa.
Sabuwar ajandar mulkin duniya da Xi Jinping ya gabatar, ta yi magana kai tsaye kan wasu muhimman abubuwa guda uku a tsarin jagorancin duniya, wato rashin daidaiton iko, da rarrabuwar ra’ayoyi, da kuma rashin daukar matakai.
Ajandar, wadda ta fitar da wasu ka’idoji guda biyar, wato tabbatar da daidaiton ikon mulkin kasa, da bin dokokin kasa da kasa, da aiwatar da ra’ayin bangarori daban-daban, da ba da shawarar kula da bukatun jama’a, da kuma mai da hankali kan aiwatar da matakai na samar da wata hanya a fayyace ga kasashen duniya ta gudanar da ayyuka cikin adalci, yayin da ake jagorancin duniya, kamar shiga ayyuka, da yanke shawara da kuma samun fa’ida.
Misali, ajandar ta jaddada cewa, “Akwai bukatar inganta wakilci da murya tsakanin kasashe masu tasowa,” wannan hakan ya dace da fatan kasashe masu tasowa na samar da tsari mai adalci. Kazalika, shawarar “Kaucewa amfani da ma’aunai biyu, wato kauracewa kakaba ‘dokokin gida’ na wasu kasashe a kan sauran kasashe”, wanda hakan ya nuna rashin amincewa da ra’ayin bangare guda daya. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp