Sabuwar hanyar kasuwanci ta duniya mai hadakar kan-tudu da teku, wacce ta kasance wata babbar hanyar hada-hadar kayayyaki da ta hada yankunan yammacin kasar Sin da kasuwannin duniya, ta fadada zuwa tashar jiragen ruwa 555 a kasashe da yankuna 127.
Mai babbar cibiyar gudanar da aiki a birnin Chongqing dake kudu maso yammacin kasar Sin, wannan hanyar ta kasuwanci ta hada hancin tasoshin jiragen ruwa na duniya ta hanyar layin dogo, da hanyoyin ruwa da manyan hanyoyi ta lardunan kudancin kasar Sin kamar Guangxi da Yunnan.
Bisa bayanan da ofishin kula da tashar jiragen ruwa da sauran hidindimu na birnin Chongqing ya fitar a yau Alhamis, an yi safarar kwantenonin kayayyaki 251,800 daga Chongqing ta sabuwar hanyar kasuwancin a shekarar 2024. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)