Tawaga ta 22 ta jamian lafiya Sinawa, ta isa Uganda domin gudanar da ayyukan dake da nufin bunkasa kiwon lafiya a kasar ta gabashin Afrika.
Guo Zhiping, shugaban tawagar, ya shaidawa Xinhua a jiya cewa, tawagar ta kunshi likitoci 7 dake da kwarewa a fannoni daban-daban da suka hada da lafiyar ciki da hanji da mafitsara da cututtuka masu yaduwa da lafiyar kunne da hanci da makogwaro da kula da marasa lafiya a dakin tiyata da sauransu.
A cewarsa, aikin tawagar ta 22 shi ne, amfani da kwarewarsu wajen kula da lafiyar alummar Uganda da ci gaba da zurfafa hadin gwiwa da shugabancin asibiti da bayar da horo da duba marasa lafiya ta hanyoyin sadarwar zamani da kiwon lafiyar alumma.
Bugu da kari, ya ce suna sa ran a shekara mai zuwa, kwararru Sinawa a fannin lafiyar manya da na tiyata da kandagarki da dakile COVID-19 da sauran cututtuka masu yaduwa da na likitancin gargajiya na Sin, za su karawa juna sani tsakaninsu da takwarorinsu na Afrika. (Mai fassara: Faiza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp