Wayewar kan kasashen Larabawa ta hada da wanzar da zaman lafiya da yin hakuri ga juna, duk wadannan sun yi kama da wayewar kai ta al’ummar Sinawa wadda ta kunshi zaman jituwa da jure bambance-bambance tsakanin juna.
Kafin kaddamar da gasar cin kofin duniya a kasar Qatar, wasu ‘yan siyasar kasashen yamma sun yi kirarin nuna adawar diplomasiyya, amma kasar Sin ta nuna goyon bayanta ga gasar ta hanyoyi daban daban, inda ta nuna matsayinta na yin adawa da yunkurin siyasantar da wasannin motsa jiki.
Hakika kasar Sin da kasashen Larabawa aminan hadin gwiwa ne bisa shawarar ziri daya da hanya daya, kawo yanzu kasar Sin ta riga ta dadddale yarjejeniyar hadin gwiwa bisa shawarar da kasashen Larabawa 20 da kuma kungiyar tarayyar kasashen Larabawa.
Yanzu ana kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu bisa shawarar ziri daya da hanya daya, da kuma wasu muradun kasashen Larabawa, alal misali tsarin samar da makamashi mai dorewa nan da shekarar 2035 na Masar, da burin Saudiyya nan da shekarar 2030, da burin kasar Qatar nan da shekarar 2030 da sauransu.
Kafin wannan, jami’ar Princeton ta kasar Amurka ta taba gudanar da wani bincike kan ra’ayin al’ummomin kasashen Larabawa guda tara da suka hada da Iraki da Jordan da Lebanon tsakanin watan Oktoban shekarar 2021 zuwa watan Aflilun shekarar 2022, sakamakon binciken ya nuna cewa, kasar Sin ta fi Amurka samun karbuwa a wajen al’ummonin kasashen Larabawa. Yanzu haka cudanyar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa ta kara karfafa a karshen shekarar bana, ana sa ran lamarin zai ciyar da hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu gaba zuwa wani sabon mataki. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)