Ƙungiyar Gudanar da Bincike da Ba da Shawarar Horo ga Ƙasashen Duniya (ITRAP), ta ce Nijeriya ba za ta iya magance matsalar cin gashin kan ƙananan hukumomi ba sai an fara magance matsalar asusun haɗin gwiwa tsakanin jihohi da ƙananan hukumomi.
Daraktan ITRAP na ƙasa, Dr Mcphalane Ejah neya bayyana hakan a wata hira da NAN a Calabar yayin da yake magana kan cin gashin kan ƙananan hukumomi.
- Hukumar Kwastam Ta Kama Tankar Mai Dauke Da Buhunan Shinkafa A Kaduna
- Babu Wata Karamar Hukumar Da Ke Ƙarƙashin Ikon Ƴan Ta’adda A Filato -Gwamna Mutfwang
Daraktan, wanda kuma mamba ne na Chatham House, ya bayyana cewa har yanzu kundin tsarin mulkin Nijeriya yana da wani sashe da ya ba da damar yin asusun haɗin gwiwa tsakanin majalisun jihohi da ƙananan hukumomi.
Ya ce hakan ya sa ya zama da wahala ga ƙananan hukumomi su zama masu cin gashin kansu kuma su samu damar gudanar da shirye-shiryen ci gaba waɗanda su ne abubuwan da suka sa a gaba.
“Har sai an soke wannan ɓangare na kundin tsarin mulki ko kuma a gyara duk wani abu da muke yi na fannin ilimi.
“Kuma za a yi hakan ne saboda a matsayinmu na al’umma, muna ci gaba da ƙoƙarin canza abubuwan da ‘yan siyasa ba sa son canzawa,” in ji shi.
Ya kuma bayyana cewa ba yau aka fara aikin gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar kan batun cin gashin kan ƙananan hukumomi ba.
Ejah ya ƙara da cewa ana sa ran kashi biyu cikin uku na ‘yan majalisar wakilai za su kaɗa ƙuri’ar amincewa ko kuma ƙin amincewa da gyaran.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Bola Tinubu ta bayar da umarnin ne kawai, biyo bayan hukuncin da kotun ƙoli ta yanke, cewa a biya kason kuɗaɗen da majalisun za su samu kai tsaye a asusunsu.
A cewarsa, wannan ba gyara ba ne, domin kuwa sai an zagaya jihohi 36 yadda al’umma za su mara masa baya kafin ya zama doka.
“Abin da muka yi shi ne yunƙurin zartarwa na ganin ƙananan hukumomi sun samu kuɗaɗensu kai tsaye amma hakan ba zai yi tasiri ba saboda tanade-tanaden hukuncin kotun ƙoli bai wuce tsarin mulki ba,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp