Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta kare ‘yancin ‘yan jarida da ke gudanar aikinsu a fadin kasar nan cikin shekaru takwas na shugabancinsa.
Buhari ya sanar da hakan ne a jiya Talata a yayin da yake taya ‘yan jarida murnar zagayowar ranar bikin ‘yan jarida ta duniya.
- Saboda Ziyarar Tinubu, Wike Ya Ba Da Hutu, Ya Umarci Rufe Kasuwanni
- Nijeriya Za Ta Yi Koyi Da Salon Ci Gaban Kasar Sin, In Ji Wani Jami’in Kasar
Ana dai gudanar da bikin zagoyowar ranar ne, a duk ranar 3 ga watan Mayun kowace shekara.
Taken taron na bana shi ne, ‘Inganta ‘yanci: Bayar da damar fadin albarkacin baki a matsayin ‘yancin dan Adam’.
Shugaban ya ce, “Mun ci gaba da bai wa ‘yan jarida ‘yancinsu, inda ya kara da cewa, mun kuma tabbatar da bai wa ‘yan Jarida ‘yancinsu don gudanar da akinsu.”
A cewarsa, “A wannan ranar da ake gudanar da bikin ‘yancin ‘yan jarida, mun ci gaba da ba su, walwalar gudanar da aikinsu har lokacin da muke shirin barin ofis.”
Buhari ya sanar da cewa, bikin na wannan shekarar yau shekaru 30 ke nan ana gudanar da bikin, tun bayan da babban zama na majalisar dinkin duniya ya faro taron, inda ya bayyana cewa, nasarar da aka samu tunawa ce ga kwararun ‘yan jarida, musamman wadanda suka sadaukar da rayukansu wajen fadarawa da kuma ilimantar da ‘yan Nijeriya.
Shugaban ya kuma yi kira ga kwararrun ‘yan jaridar da ke kasar nan kar su gajiya wajen ci gaba da nuna kishin kasa a yayain gudanar da aikinsu, musamman don hada kan kasa, inda kuma ya bukace su da su dinga wanzar da ‘yancin nasu bisa ka’ida.