Yayin da gwamnatinsa ke bankwana, shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa ya yi iya kokarinsa wajen yi wa Nijeriya hidima.
A sakonsa na sabuwar shekara ta 2023 ga ‘yan Nijeriya, Buhari ya bayyana fatansa na cewa shugaban kasa mai jiran gado zai karbi mulki cikin nasara.
- Tashoshin Talabijin 6 Zasu Haska Shiri Na Musanman Kan Rayuwar Shugaba Buhari
- Shugaba Buhari Ya Amince Da Siyo Motocin Sulke Don Yaki Da ‘Yan Ta’adda
A cewarsa, “yayin da muke maraba da sabuwar shekara, mun sa ido da fatan 2023, ta zama shekarar da z amu samu ci gaba a matsayin al’umma domin samun hadin kai, ci gaba da wadata.
” Ina addu’ar shugaban kasa mai jiran gado shi ma ya karbi kasar ya ci gaba da fafutukar ganin Nijeriya ta kasance cikin sahun gaba a duniya nan da wani dan lokaci.”
Shugaba Buhari ya ce kowace sabuwar shekara wata dama ce ta yin tunani a kan shekarar da ta wuce, a sabanta shugabanni da kuma ci gaba.
A yayin da muke murnar shiga sabuwar shekarar 2023, shugaban kasar ya yi ta’aziyya ga ”Yan uwanmu ‘yan Nijeriya da suka rasu.
Ya ci gaba da cewa wannan shekarar tana da matukar muhimmanci a gare shi domin a shekarar ne zai bankwana da shugabancin kasar.