Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf Kabir ya bukaci mazauna jihar da su rungumi halayen tausayi, karamci, da’a, kishin kasa, da zaman lafiya domin ci gaban jihar da kasa baki daya.
A cewar Gwamnan a sakonsa na Sallah a Kano ranar Laraba, ya kamata kowa ya ci gaba da koyi da irin wadannan kyawawan halaye har gaban watan Ramadan.
- Sakon Sallah: Gwamna Nasir Ya Yi Kira Da Hadin Kai Don Gina Jihar Kebbi
- Sallah: Gwamnatin Katsina Ta Yi Wa Fursunoni 222 Afuwa
A yayin da yake taya daukacin al’ummar jihar da Shugaba Bola Tinubu da daukacin al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan, Gwamnan ya sake nanata aniyarsa ta cika alkawuran da ya dauka yayin yakin neman zabensa.
Gwamna Abba Yusuf ya bayyana kwarin gwiwar cewa, ‘bayan wuya sai daɗi’, inda yace, gwamnatinsa ta shirya aiwatar da manyan ayyukan raya kasa a shekarar 2024.