Ɗan wasan gaban ƙasar Masar dake wasa a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool Mohamed Salah, ya rattaba hannu kan sabon kwantiragin shekaru biyu da Liverpool, tsohon kwantiragin ɗan wasan zai kare a wannan kakar ta bana inda aka yi shakkun cewa zai ci gaba da zama a Anfield sakamakon kalaman da ɗan wasan mai shekaru 32 ya yi a kakar wasa ta bana da kuma raɗe-raɗin da ke alakanta shi da komawa Saudiyya.
Sai dai a yanzu ta tabbata tsohon ɗan wasan na Chelsea zai cigaba da zama a Liverpool inda ya zura kwallaye 243 sannan ya taimaka aka ci 109 a wasanni 394 da ya buga, “Hakika ina matukar farin cikin kasancewa tareda babbar kungiya a yanzu,” in ji Salah.
- Arsenal Ta Matsawa Liverpool Ƙaimi Bayan Doke Tottenham A Emirates
- Yaushe Liverpool Za Ta Lashe Gasar Firimiyar Ingila?
“Ina fatan lashe manyan kofuna tare da Liverpool sannan kuma ina fatan cigaba da jin daɗin wasa anan, na buga wasanni shekaru takwas a nan, da fatan zasu zama 10, Ina jin daɗin rayuwata a nan, ina jin daɗin ƙwallon ƙafa. Na yi shekaru mafi kyau a rayuwata a nan” ya ƙara da cewa.
Salah ya ci kwallaye 32 a dukkanin gasa a kakar wasa ta bana, ciki har da 27 a gasar Firimiya yayin da Reds ke neman lashe gasar karo na 20, Liverpool ta ba Arsenal dake matsayi na biyu maki 11 inda ake da sauran wasanni bakwai, Salah, wanda ya koma Liverpool daga Roma a shekarar 2017, ya lashe Kofin Zakarun Turai, Premier League, Kofin FA, League Cup da Fifa Club World Cup tare da Reds.
Ya kasance ɗaya daga cikin manyan ‘yan wasan Liverpool uku da kwantiraginsu zai kare a wannan bazarar, tare da mai tsaron baya Trent Alexander-Arnold da kuma ɗan wasan baya na tsakiya Virgil van Dijk.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp