Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da Masar, Mohamed Salah, ya yi kira ga shugabannin kasashen duniya da su taru domin hana ci gaba da kashe rayukan da ba su ji ba, ba su gani ba, a rikicin Isra’ila da Palestinawa.
Salah, mai shekaru 31, ya ce dole ne a ba da damar kai agajin jin kai zuwa ga Gaza nan take.
- Shin Salah Zai Iya Barin Liverpool Zuwa Gobe?
- Wike Ya Ƙaryata Batun Rushe Wani Ɓangare Na Masallacin Kasa Da ke Abuja
Jami’an kiwon lafiya sun ce daruruwan mutane ne suka mutu sakamakon fashewar wani abu a wani asibiti mai cunkoson jama’a a birnin Gaza a daren Talata inda akalla mutane 500 suka mutu kuma yawanci mata da kana nan yara da kuma mata masu ciki.
Sai dai rundunar sojin Isra’ila ta dora alhakin kai harin ga kungiyar Jihad ta Islama ta kasar Falasdinu.
Sama da mutane 3,000 ne aka bayar da rahoton cewa an kashe a hare-haren da aka kai a Gaza tun ranar 7 ga wannan watan.
Salah ya bayyana abubuwan da ke faruwa a Gaza a matsayin abin ban tsoro wanda ke bukatar dauki.
“Mutanen Gaza na bukatar abinci, ruwa da magunguna cikin gaggawa” in ji Salah, a wani faifan bidiyo da ya saka a kan shafinsa na X.
Salah ya cigaba da cewa “dukkan rayukan mutanen Gaza dole ne a kiyaye su, ana bukatar a daina kashe-kashen jama’a ana raba iyalai da ‘yan uwansu”
Tuni dai kasar Masar ta bude mashigar Rafah, domin shigar da manyan motoci 20 dauke da kayan agaji zuwa Gaza.