Gwamnatin jihar Kaduna, na ci gaba da kulawa da almajirai a jihar kamar yadda ta yi alƙawari inda ta shirya cin abinci da almajiran a jiya Asabar, albarkacin bikin babbar sallah.
Mai bai wa gwamnan shawara kan shirin ciyar da abinci a makarantu, Hajiya Fauziyya Buhari Adam, ce ta bayyana haka a wata ziyara da ta kai makarantar kwana ta almajirai a ranar Sallah, mai suna ‘Umaru Musa ‘Yar Adua Almajirai Bilingual Model Primary School’, da ke karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna, wanda ta ce hakan ne ya sa gwamnatin ta shirya musu cin abincin sallah domin su ji cewa lallai ta san da su.
- Sojojin Sama Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 100, ‘Yansanda Sun Ceto Mutanen Da Aka Sace A Katsina
- Suyar Naman Sallah Ta Musamman
Hajiya Fauziyya yayin da ta ke ƙarin haske kan manufofin gwamnatin Uba Sani, musamman kan makarantun tsangaya da almajirai, ta nuna cewa za su ci gaba da tallafawa makarantun kwana na almajirai a fadin jihar domin ganin yadda za a zaburar da malamai dan sauke nauyin da ke kansu.
Shugaban makarantar Abdulhamid Aliyu, ya ce su na da kimanin dalibai 500, inda ya yi godiya da addu’a ga gwamnatin Kaduna na canji da suka gani ta bangaren ciyarwa da kulawa.
Su ma Iyaye da wasu cikin almajiran makarantar sun bayyana jin dadin su kan kulawar gwamnatin jihar Kaduna take da harkokin iliminsu.