Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya karbi bakuncin Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa, a taronta na kwamitin zartarwa karo na 7, a Maiduguri ranar Talata, inda ya jaddada cewa, samarwa matasa abun yi a fadin Arewa zai magance matsalar rashin tsaro da ke addabar al’ummar yankin.
Taron mai taken “Inganta Tsaro A Matsayin Ginshikan Hanyar Haifar da Dawwamamman ci gaban Arewa”, Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, wanda Gwamna Zulum ya wakilta ne ya bude taron.
- CMG Ta Kulla Yarjejeniyar Hadin Gwiwa Da Gidan Talabijin Na Kasar Vietnam
- Minista Ya Gargaɗi Jami’an Gwamnati Kan Rashin Sanin Ilimin Tantance Ingantattun Labarai
Gwamnan ya bayyana tsaro da samar da zaman lafiya, noma da samar wa matasa sana’o’in dogaro da ka a matsayin ginshikan ci gaba mai dorewa a yankin arewa.
Zulum ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki da su maida hankali wajen samar da damammaki ga matasa a arewacin Nijeriya.
A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Sarakunan Arewa kuma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya bayyana cewa, taron da aka yi a Jihar Borno an yi shi ne domin karfafa hadin kan jihohin Arewa da kuma tattaunawa kan halin da yankin ke ciki domin tallafa wa shugabannin siyasa wajen magance matsalolin da ke addabar Arewa.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) da babban hafsan tsaro (CDS) da babban sufeton ‘yansanda (IGP) duk sun samu wakilci a taron sarakunan.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Arewa kuma gwamnan jihar Gombe, Mohammed Inuwa Yahaya, wanda mataimakinsa, Manassa Daniel Jatau ya wakilta; Sanata Kaka Shehu Lawan; Shehun Borno, Abubakar Umar Garbai, da sauran sarakunan gargajiya da dama a fadin jihohin Arewa 19.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp