Shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Amurka Joe Biden, sun yi musayar ra’ayoyi mai zurfi, a rukunin gidajen alfarma na Filoli dake birnin San Francisco na kasar Amurka ranar Laraba. Taron kolin da aka dade ana jira, na zuwa ne shekara guda bayan ganawar shugabannin biyu a tsibirin Bali na kasar Indonesia.
A jawabinsa yayin ganawar shugaba Xi ya jaddada cewa, kasar Sin ta dukufa wajen samun daidaito, da dorewar dangantakar lumana da kasar Amurka. A lokaci guda kuma, kasar Sin tana da moriya da ka’idojin da suka kamata a kiyaye, da jan layin da ba za a iya ketarewa ba.
Kasar Sin na fatan kasashen biyu za su kasance abokan hulda masu mutunta juna da zaman tare cikin lumana. Taron dai ya kasance wani muhimmin zabi mai muhimmanci ga kasar Sin, don daidaita dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma halin da ake ciki a duniya.
Masanin tattalin arziki na kasar Amurka Jeffrey Sachs ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, ra’ayin mutunta juna, da yin hadin gwiwa,da tattaunawa, da warware matsaloli tare, akwai “hikima sosai”, a cikinsa kuma yana da matukar muhimmanci.
Yana mai cewa, hadin gwiwar Sin da Amurka ba wai kawai kan muradun bai daya ne na kasashen biyu ba, yana kuma nuni da wani nauyi da ya rataya a wuyan kasashen duniya. A yayin taron, shugaba Xi ya yi kira ga kasashen biyu, da su hada kai a matsayinsu na manyan kasashe, yana mai jaddada cewa, za a iya magance matsalolin da ke addabar bil-Adama ne kawai ta hanyar hadin gwiwa tsakanin manyan kasashe.
Yarjejeniyar da aka cimma a yayin taron na San Francisco, ta nuna cewa, kasashen biyu suna da moriyar bai daya, kuma za su iya yin hadin gwiwa don samun sakamako mai tarin yawa. Dangantakar Sin da Amurka mai dorewa ba tunanin fata ba ne. Don haka, ya bukaci kasashen biyu su yi aiki tare.
Kuma tattaunawa shi ne mataki na farko na amincewa da juna, da mutunta juna da kuma hada kai. Daga Bali zuwa San Francisco, babban jirgin ruwa na hadin gwiwar kasashen Sin da Amurka, ya yi tattaki ta cikin duwatsun teku da kadawar igiyar ruwa. Amma ba a San Francisco za a tsaya ba. Birnin, wanda ya shaida tarihin musanya tsakanin Sinawa da Amurkawa na tsawon karni, wani sabon mafari ne na dangantakar kasashen Sin da Amurka. (Ibrahim)