Malama Safiya Yakubu, wata matashiya ce mai sana’ar kitso irin na zamani da ke zaune a Karamar Hukumar Suleja ta Jihar Neja ta bayyana sana’ar kitso a matsayin sana’ar da ta inganta rayuwarta ta har ta kai ga tana tallafa wa wadansu. Ta bayyana haka ne a tattaunawarsu da wakiliyar LEADERSHIP HAUSA MARYAM ga yadda hirar tasu ta kasance:
Masu karatu za su so sanin sunanki?
Suna na Safiya Yakubu
Safiya ‘yar kasuwa ce ko ma’aikaciyar gwamnati, ko kuma dai ana taba wata wata sana’a ce?
Eh to gasliya muna taba sana’ar hanu ce
Wace Sana’a kike yi?
Ina sanaa’r kitso ne
Masha Allah, to a ina kike sana’ar?
Ina Sana’ata ne a gida
Kin kai kamar shekara nawa da fara wannan Sana’a?
Gaskiya na dade sosai da fara wannan sana’a don zai kai kimanin shekara takwas ina yi.
Kafin ki fara wannan sana’a kina wata sana’ar ce?
Eh ina sana’ar sayar da gawayi
Ita sana’ar gawayin har yanzu kina yi ko kin ajiye ta?
Eh ina dan tabawa kadan-kadan don jarin ya kan tsinke don yau da kullum, amma kitso ba sai da jari ba.
Wane ci gaba kika samu a wannan sana’a taki?
Alhamdulillah, a wannan kana’a na samu ci gaba sosai saboda da wannan sana’a har na sayi freezer guda biyu wanda na ke sayar da ruwan leda “Pure Water” da kuma lemu kuma har na samu wadanda suka zo koyon kitso a guri na.
Ko kina da wani kuduri don sake bunkasa sana’ar taki?
Eh ina so in bude shago yanzu saboda mutane su na yi mun yawa sosai musamman lokacin bukukuwa kamar Sallah, suna ko biki.
Kimanin Mutane nawa ke karkashinki?
Yanzu haka ina da yara uku karkashina, kuma Alhamdu lillahi suna kokari sosai don har kunshi ma suna yi wani lokaci cika gidan ke yi da masu gyaran kai.
Kamar nawa kike samu a rana?
To ya danganta da yawan mutanen da na yi wa kitso na kan samu kimanin dubu shida ko biyar
A karshe wane kira kike da shi ga masu irin taki sana’ar da sauran sanao’i?
Ina kira ga duk masu sanao’i da su rike gaskiya, kuma su rike sana’arsu tsakani da Allah don shi kadai ne zai taimake su kuma a daina zaman kashe wando, yanzu sai ka ga mutum da karatunsa amma bai da aikin yi inda sana’ar hannu ai ba sai ya je ya yi roko ba. Allah ya sa mu dace.