Yayin da aka shiga lokacin girbin tuffa a kayuyen Nangou na birnin Yan’an dake lardin Shaanxi na arewa maso yammacin Sin, a ranar Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yawata a cikin gonar tuffa domin fahimtar yadda aikin girbi na bana ke gudana.
Yayin rangadin, Shugaba Xi ya gano yadda fasahar ban ruwa da na tantance ’ya’yan itatuwa a kauyen Nangou ke ci gaba da samun tagomashi, inda ya yaba da yadda aka raya sana’ar shuka tuffa, wadda ta kasance a sahun gaba, kuma mai kyakkyawar makoma.
Har ila yau, Xi ya jaddada cewa, wajibi ne a inganta farfado da yankunan karkara da aiki tukuru domin cimma zamanantar da ayyukan gona da yankunan karkara. (Fa’iza Mustapha)