An yi cikakken zama na biyu na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20 daga ranar 26 zuwa 28 ga watan Fabrairun shekara ta 2023 a Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ne ya shugabanci taron, inda babban sakataren kwamitin, Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi.
A yayin zaman, an saurara gami da tattauna rahoton aikin da Xi Jinping ya gabatar a madadin ofishin siyasar, da dubawa gami da amincewa da takardar jerin sunayen mutanen da aka bada shawarar su zama shugabannin hukumomin kasar Sin, da ofishin siyasar ya yi shirin gabatarwa ga zama na farko na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14. Haka kuma, akwai takardar jerin sunayen mutanen da aka bada shawarar su zama shugabannin majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar, da ofishin siyasar ya shirya gabatarwa ga zama na farko na majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar karo na 14. Duk wannan ya gudana ne bayan ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ya saurari ra’ayoyi daga ciki da wajen jam’iyyar kwaminis, tare kuma da yin shawarwari cikin tsanaki, daga bisani kuma aka yanke shawarar gabatar da wadannan takardun biyu zuwa ga tawagar shugabannin zama na farko na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14, gami da na zama na farko na majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar karo na 14.
Har wa yau, a yayin zaman, an duba gami da amincewa da shirin yin garambawul ga hukumomin jam’iyyar kwaminis da na kasa, bisa tushen tattaro ra’ayoyin bangarori daban-daban. Shugaba Xi ya yi karin haske kan daftarin shirin a wajen cikakken zaman, inda aka amince da a gabatar da wasu tanade-tanaden shirin bisa matakan doka, zuwa ga zama na farko na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14, don a duba su. (Murtala Zhang)