A yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce hadaddiyar sanarwar da aka fitar a gun taron ministocin harkokin waje na kungiyar G7 ba ta da tushe, inda ta zargi kasar Sin, ta kuma tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasar. Don haka Sin ba ta amince da sanarwar ba.
Rahotanni na cewa ministocin harkokin wajen kasashe membobin kungiyar G7, sun tattauna damuwar da ake nunawa game da fadada karfin soja, da makaman nukiliya na kasar Sin, inda suka ce suna bukatar bangaren Sin ya yi alkawarin kiyaye zaman lafiya.
Game da hakan, Lin Jian ya ce Sin kasa ce da ta fi mayar da hankali ga batun kiyaye zaman lafiya da tsaro, tana kuma tsayawa tsayin daka kan turbar samun ci gaba cikin lumana, da manufofin kiyaye tsaron kasa, da na kiyaye takaita yawan makaman nukiliya bisa bukatun tsaron kasar.
Jami’in ya ce kungiyar G7 ba ta ambato alhakin dake wuyan kasar Amurka, na rage makaman nukiliya, da hadarin yaduwar makaman nukiliyar a sakamakon raya dangantakar abota, ta kiyaye tsaro a tsakanin Amurka da Birtaniya da Australia ba, amma ta zargi kasar Sin ba tare da wani tushe ba. (Zainab Zhang)














