Kwamishinan ‘yansandan jihar Kano, Salman Dogo Garba, ya ce ‘yansanda sun kama wani da ake zargi tare da samun nasarar kwato wasu abubuwa da suka hada da bama-bamai, biyo bayan sanarwar da hukumar ta fitar kan zargin kai harin ta’addanci a jihar.
Da yake magana a wani taron manema labarai a ranar Litinin, CP Dogo ya bayyana matakan da ‘yansanda suka dauka a jihar don tabbatar da tsaron dukiyoyi da rayukan mazauna jihar da kuma dakile duk wata barazana.
- Hisbah Ta Ceto Ƴanmata 16 Daga Hannun Masu Safarar Mutane A Kano
- Kwankwaso Ya Soki Ƴansandan Kano, Ya Buƙaci A Girmama Ƴancin Kano
“Kwanan nan, mun fitar da sanarwa game da yiwuwar kai harin ta’addanci a Kano, musamman a lokacin taron Mauludin Shehu Ibrahim Inyass. Mun yin shela, mun sanar da jama’a, tare da samar da kayan aiki don shawo kan lamarin,” in ji CP Garba.
Ya bayyana cewa, wadanda ake zargin sun tsere daga jihar biyo bayan tona musu asiri, amma an cafko daya an dawo da shi Kano bayan ya tsere da farko.
CP Dogo, ya jaddada mahimmancin samun rahoton leken asiri wajen dakile barazanar da ake iya fuskanta, tare da yin cikakken bayani kan yadda ‘yansanda suka hada kai da masu ruwa da tsaki don inganta tsaro a lokacin taron.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp