Sanata Ibrahim Lamido mai wakiltar mazabar gabashin Sokoto, ya bayar da tallafin karatu na Naira miliyan 40 ga dalibai marasa karfi 1,315 daga mazabarsa, wadanda ke karatu a fannoni daban-daban a jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto.
Lamido, da yake jawabi ga daliban da suka amfana da shirin a Sokoto, ya ce hakan na daga cikin kudurinsa na rage radadin talauci da ake fama da shi a mazabarsa.
Sanatan wanda ya samu wakilcin Malam Sani Bala, ya ce, “An tantance daliban ne ta hanyar wani kwamiti a dukkanin gundumomin da ke yankin Gabashin jihar.
“An zakulo daliban da suka amfana da shirin ne ta hanyar yin bincike mai zurfi, za a tura wa daliban da suka amfana da tallafin kudadensu da zarar an kammala tattara bayanansu.
“Daliban da aka tantance ana sa ran za su biya jami’ar sama da Naira miliyan 80, wanda tuni gwamnatin jihar ta biya rabin kudin. Yanzu kuma, Sanata Lamido ya biya rabin don ci gaba da karatun daliban,” inji shi.
Wasu daga cikin wadanda suka amfana da shirin, wadanda suka zanta da manema labarai, sun bayyana tallafin a matsayin wani irin ceton rayuwa don ci gaba da harkokin karatunsu.