Kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP ta zaɓi tsohon shugaban majalisar dattawa ta ƙasa kuma tsohon gwamnan jihar Kwara, Dr Abubakar Bukola Saraki a matsayin wanda zai jagoranci kwamitin samar da gyara da lalubo hanyoyin ci gaban jam’iyyar.
Shugaban ƙungiyar kuma gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ne ya bayyana haka a hirarsa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron da aka yi a gidansa da ke babban birnin tarayya Abuja.
- Kantoma Na Ƙaramar Hukumar Shira Ya Rasu Kwanaki Kafin Zaɓen Cike Gurbi
- Sojoji Sun Cafke Dillalan Sayar Da Bindigu A Filato
A cewarsa, an kafa kwamitin mutum bakwai da za su jagoranci sasanta rikicin jam’iyyar da kuma ba wa waɗanda aka ɓatawa haƙuri tare kuma da shirya taron masu ruwa da tsaki na jam’iyya wanda za a yi ranar 27 ga wannan watan na Mayu.
Saraki, shi ne zai jagoranci kwamitin sai kuma ƴan kwamitin da suka haɗa da gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare; gwamnan jihar Filato, Caleb Muftiwang da kuma gwmanan jihar Enugu, Peter Mba.
Sauran ƴan kwamitin sun haɗa da Sanata Seriake Dickson da Sanata Ibrahim Dankwambo da tsohon gwamnan jihar Abia, Chif Okezie Ikpeazu.
Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da gwamnonin Enugu da Zamfara da Adamawa da Taraba da Osun da Oyo.
Ministan babban birnin tarayya Abuja kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyeson Wike shima ya je taron sai kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Maƙarfi.
Suma ƴan jam’iyyar irin su Sanata Aminu Waziri Tambuwal da Sule Lamido da Samuel Ortom da Gabriel Suswan da Seriake Dickson da Sam Egwu da Liyel Imoke da Achike Udenwa da Olagunsoye Oyinlola da Adamu Muazu da kuma Idris Wada duka sun halarci taron.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp