Shugaban Jam’iyyar NNPP na Jihar Kano, Hashimu Sulaiman Dugurawa ya ce sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna hudu masu daraja ta daya wanda suka hada da sarakunan Gaya, Rano, Karaye da Bichi ba su da maraba da kwamishinoni, wadanda tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullai Umar Ganduje ya nada domin su taimakamasa cin zabe a 2023.
Dugurawa ya bayyana haka ne alokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa. Ya ce wata gidoga ce da aka shirya domin ta kare faduwar gwamnatinsa, wanda kuma daga karshe ta fadi zabe.
Shugaban jam’iyyar ya ci gaba da cewa sarakunnan sun yi amfani da mukamansu daga Gwamnatin Ganduje, ya kara da cewa wannan al’amarin na al’umma ne suke fatan samun wata daraja bayan karewar Gwamnatin Ganduje.
- An Jinjinawa Matakan Kare Hakkin Bil Adama Na Kasar Sin Yayin Zaman Taron MDD
- Kanana Hukumomin Kano Da Jigawa 23 Na Kan Gaba Wajen Fuskantar Ambaliyar Ruwa – NEMA
“Sarakunan masu daraja ta daya da muka samu a kan karagar mulki ba wasu ba ne illa kwamishinoni da Ganduje ya nada domin su taimake shi cin zaben shekara ta 2023. Sun taka rawa kuma sun fadi, saboda haka zangonsu yakare yanzu.
“Abin da ya kamata shi ne, tun da Ganduje ya fadi zabe kuma ya sauka daga matsayin Gwamnan Jihar Kano, kamata ya yi suma su gaggauta barin kujerunsu, domin ba wanda zai hau kujerar sarkin Kano tun da Sarki Muhammadu Sanusi II ya bar ta.
“Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf na yin aiki bisa abin da al’ummar Kano ke bukatar, sannan kuma akwai gurbin kujerar sarkin Kano wanda hakan tasa aka sake nada Sarki Muhammadu Sanusi II, wanda aka sauke tun da farko. Wannan tasa majalisar dokokin Jihar Kano ta yi wa dokar masarautar gyara, sannan kuma gwamna ya rattaba mata hannu.”