BBC ta rawaito cewa, Sarki Charles na uku zai sayar da wasu daga cikin dawakan da ya gada daga mahaifiyarsa Sarauniya Elizabeth II.
Marigayiya Sarauniya ta kasance mai son dawaki kuma tana kiwonsu.
- Alakar Sarauniya Elizabeth II Da Nijeriya
- Za A Sauko Da Tutar Nijeriya Kasa Don Girmama Sarauniya Elizabeth
Gidan gwajon kayayyaki na Tattersalls ya ce zai yi gwajon dawaki 14 na Sarauniya a yau Litinin.
Daga cikin dawakin har da Just Fine wanda ya lashe tsere kusan 100.
Kakakin gidan gwajon na Tattersalls ya ce ba wani sabon abu bane saboda a duk shekara suna sayar da dawaki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp