Sarkin Zulu na Afirka ta Kudu, Misuzulu kaZwelithini, ya musanta zargin da ake yi cewa watakila an ba shi guba, yana mai cewa yana cikin koshin lafiya.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake takaddama bayan da firaministansa na gargajiya ya fada a karshen mako cewa sarkin na jinya a Eswatini bisa zargin ya ci guba.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 4 Da Ceto Mutum 24 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Zamfara
- ‘Muhallin Mutum 43,000 Aka Cunkusa Alhazan Nijeriya 95,000 A Mina’
Cif Mangosuthu Buthelezi ya ce sarkin na kwance a asibiti sakamakon mutuwar daya daga cikin manyan mashawartansa, wanda kuma ake zargin shi ma guba ce ta kashe shi, amma mai magana da yawun sarkin ya musanta hakan inda ya ce yana cikin koshin lafiya.
Cikin faifan bidiyon da aka raba wa manema labarai na Afirka ta Kudu, sarkin ya ce an tsara zai dinga zuwa duba lafiyarsa akai-akai, wanda ya yanke shawarar yi a Eswatini.
“Ni ban ci wata guba ba, ina cikin koshin lafiyata 100 bisa 100.
“Ina cikin farin ciki saboda ina da koshin lafiya, babu wata guba da na ci. Don haka mutane, al’ummar Zulu, da dangina su tunatar da jama’a cewa kada a saurari duk abin da mutane ke fadi, ”in ji shi.
An kuma ambato Sarki Misuzulu yana shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP ta wayar tarho daga Eswatini cewa “yana cikin koshin lafiya sosai”.
Sarkin mai shekara 48 ya hau karagar mulki a shekarar da ta gabata bayan rasuwar mahaifinsa Sarki Goodwill Zwelithini a wani zazzafan rikici da ya barke kan gadon sarautar.