Sarkin Kudan, Malam Muhammad Bello Haladu ya taya mai martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli murnar cika shekara 3 a kan karagar mulkin Masarautar Zazzau da ke Jihar Kaduna.
Sanarwar da ta fito daga Wakilin Yada Labarun Masarautar Kudan, Malam Yusuf Ibrahim Kudan, ta bayyana cewa, sarkin, Muhammad Bello Haladu ya bayyana cewa kasancewar mai martaba Ambasada Bamalli a kan karagar mulkin Zazzau ta kawo ci gaba mai dimbin yawa ba kawai a masarautar ba har da Jihar Kaduna da ma kasa baki daya.
- NDLEA Ta Cafke Wani Tsoho Mai Shekaru 67 Dauke Da Hodar Ibilis A Filin Jirgin Saman Abuja
- NPFL: Kano Pillars Ta Doke Katsina United A Kano
Ya yi addu’ar Allah ya kara yaukaka dangantaka mai dorewa tsakanin Masarautar Zazzau da sauran masarautun da ke fadin kasar nan domin samun ci gaba mai ma’ana.
Sarkin na Kudan ya kuma bayyana kudirinsa na ci gaba da ba da goyon baya ga hakiminsa da sauran hakimai na Masarautar Zazzau baki daya.
Daga karshe Muhammad Bello ya roki al’ummar Masarautar Kudan su ci gaba da zama lafiya da juna domin samun ci gaba ba tare da la’akari da bambancin kabila, addini ko siyasa ba.