Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Nijeriya, Mai Martaba Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bayyana ranar Talata 29 ga Afrilu, 2025 a matsayin ranar farko ta watan Zulki’ida 1446AH.
Wannan sanarwar ta fito ne a cikin wata sanarwa da Wazirin Sokoto kuma shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na Majalisar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali Junaidu ya fitar a ranar Litinin.
- Kasar Sin Za Ta Samar Da Dokar Da Ta Shafi Raya Kasa
- Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci Ta Yaba Wa Gwamna Lawal Kan Matakan Yaƙi Da ‘Yan Bindiga A Zamfara
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Sanarwar ta biyo bayan rashin samun wani rahoto mai inganci daga kwamitin ganin wata na kasa da kuma kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na Majalisar Sarkin Musulmi dangane da ganin jinjirin watan a ranar Lahadi, 27 ga Afrilu, 2025.
“Saboda haka, Litinin 28 ga Afrilu, 2025, za ta kasance 30 ga Shawwal 1446AH, yayin da ranar Talata 29 ga Afrilu, 2025 za ta zama farkon watan Zulki’ida 1446AH.”
Sanarwar ta ci gaba da cewa, Sarkin Musulmi na mika sakon fatan alheri ga al’ummar Musulmi, ya kuma bukace su da su ci gaba da yi wa kasa addu’ar zaman lafiya, hadin kai, da ci gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp