Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli ya nada Alhaji Umar Abubakar Sadik a matsayin Ardon Zazzau, wanda taron nadin ya gudana a fadar sarkin Zazzau jim kadan bayan kammala sallar Juma’a.
Bayan ya kammala nadin sabon Ardon Zazzau, Malam Ahmed Bamalli ya gabatar da jawabi, inda ya yi kira ga sabon Ardon da ya rike amanar da aka dora masa na rungumar duk wasu al’ummar Fulani da suke Masarautar Zazzau. Ya kuma tuna-tar da sabon Ardo da ya rike wannan matsayi da aka nada shi da gaskiya a duk lo-kacin da ya tashi fuskantar wata matsala da ta shafi al’ummar Fulani da suke masarautar Zazzau.
- Yadda Qatar Ta Zo Da Sabon Salo Na Ba-zata A Gasar Cin Kofin Duniya
- Shugaban Kasar Sin Ya Yi Shawarwari Da Takwaransa Na Kasar Cuba
Sarkin Zazzau ya kuma tunatar da sabon Ardon Zazzau da ya rika gudanar da binciken da ya dace ga kowacce matsala da ta kasance a gabansa wanda zai tallafa masa wajen warware matsaloli da ta kasance a gabansa.
Sabon Ardon Zazzau ya lashi takobin rungumar wannan sarauta da amanar da mai martaba Sarkin Zazzau ya danka masa da hannu biyu, domin kawo karshen matsalolin da suke addabar al’ummar Fulani da ke masarautar Zazzau baki daya.
Ardon Zazzau ya kuma bayyana cewa kasancewarsa shi sanau ne kan matsalolin Fulani a masarautar Zazzau da ke Jihar Kaduna da kuma Nijeriya baki daya, na yadda ya shafe fiye da shekara arba’in a cikin kungiyar Miyetti Allah tun daga karamar hukumar Zariya ya zuwa sassan Nijeriya baki daya, zai yi amfani da wan-nan dama da yake da shi wajen tunkarar ayyukan da mai martaba sarkin Zazzau ya dora masa.