Sarkin Zazzau, Ambasada Nuhu Bamalli ya damuwarsa dangane da yawaitar ta’ammali da miyagun kwayoyi a yankin masarautarsa.
Sarkin ya ce masana harkokin magunguna sun bayyana Zazzau a matsayin garin da ya fi kowanne gari a Arewacin Nijeriya sayarwa da raba miyagun kwayoyi.
Sarkin Zazzau wanda ya bayyana haka a ta bakin Wazirin Zazzau, Alhaji Muhammadu Inuwa Aminu, a jawabin da ya gabatar yayin gudanar da taron lacca na watan azumin Ramadan wanda Gidanuniyar Sabil ta shirya a dakin taro ma gidan Sardauna da ke Jihar Kaduna.
- NDLEA Ta Kuduri Aniyar Fatattakar Masu Safarar Miyagun Kwayoyi – Marwa
- Majasirdin Sarkin Zazzau, Alhaji Yusuf Saleh Barde Ya Rasu
“Kwanan baya kungiyar masu yin magunguna sun kawo mai martaba sarki ziyara, inda suka tabbatar masa da cewa Zazzau ita ce cibiyar rarraba miyagun kwayoyi a fadin arewacin Nijeriya. Wannan bayani nasu ya girgiza mai martaba kuma ya nuna damuwarsa kan jin wannan batu. Sarki ya ba su tabbacin masarauta za ta yi iya bakin kokaranta wajen ganin an rage yaduwar miyagun kwayoyin.
“Mai martaba ya so ya halarci wannan taron, amma taron ya zo daidai da na gidan talabijin NTA wanda su ne suka fara aiko da katin gayyata wanda hakan ya sa na wakilce shi a wurin wannan taron.”
A nasa jawabin tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Dakta Mukhtar Ramalan Yero, ya bukaci iyaye da su kara zage damtse wajen kula da tarbiyyar ‘ya’yansu wanda yana daya daga cikin hakkokinsu da Allah ya dora musu.