Da misalin karfe 8 da mintuna 11 na safiyar yau Talata, sashen dawowa na kumbon Shenzhou-16 mai dauke da ‘yan sama jannati, ya sauka a filin sauka na Dongfeng lami lafiya. Bayan ’yan sama jannati guda uku da suka hada da Jing Haipeng, Zhu Yangzhu, da Gui Haichao suka fita daga kumbon, likitoti sun duba lafiyarsu, inda suka tabbatar da cewa, suna cikin koshin lafiya. Daga bisani, an sanar da cewa, kumbon Shenzhou-16 ya cimma nasarar gudanar da ayyukan sararin samaniya kamar yadda aka tsara.
A ranar 30 ga watan Mayu na bana ne, aka harba kumbon Shenzhou-16 zuwa sararin samaniya daga cibiyar harba tauraron dan adam ta Jiuquan, daga bisani kuma, kumbon ya hade da cibiyar Tianhe a tashar sararin samaniyar kasar Sin. ’Yan sama jannati guda uku sun yi aiki na tsawon kwanaki 154 a cikin tashar, inda suka yi aiki a wajen kumbon sau daya, da kuma ba da darasi daga tashar sararin samaniya karo na 4, kana, sun sha aiwatar da ayyukan fitar da na’urori daga tashar sararin samaniya, wadanda suka taimaka wajen aiwatar da ayyuka a cikin tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin ta yau da kullum.
Aikin na wannan karo, shi ne aiki na farko na harba kumbo mai dauke da ‘yan sama jannati da aka yi, tun bayan aka shiga mataki na biyu na aikin kafa tashar binciken sararin samaniyar kasar Sin. ’Yan sama jannati da kwararrun dake doron duniyarmu, sun yi hadin gwiwa wajen yin gwaje-gwajen kimiyya da fasaha kan fannonin kiwon lafiya, da fasahohin halittu, da na sararin samaniya da sauransu. Matakin da ya kasance muhimmin sauyi daga bullo da shirye-shiryen binciken sararin samaniya zuwa aiki da shirye-shiryen da aka kafa, da kuma muhimmin sauyi daga zuba jari zuwa samar da kayayyaki. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)