Ma’aikatar kula da harkokin masana’antu da sadarwa ta kasar Sin ta ba da alkaluma a yau Talata cewa, a bara, yawan matsakaitan masana’antu ya kai kashi 5.8%, wanda ya karu da kashi 1.2% bisa na makamancin lokacin na shekarar 2023, kana ma’aunin sashen masana’antun samar da kayayyaki na Sin ya nuna sashen ya ci gaba da zama kan gaba a duniya cikin shekaru 15 a jere.
A shekarar 2024, 39 daga cikin manyan nau’o’in masana’antun Sin 41 sun ci gaba da samun bunkasa ba tare da tangarda ba, inda aka daga matsayin karfin kirkire-kirkire na na’urorin zamani da na fasahar AI da dai sauran bangarori.
Baya ga haka, sauran sha’anoni masu tasowa ciki har da sabbin kayayyaki, da aikin kere-kere da halittu da sinadari, da mutum-mutumin inji da sauransu na karuwa cikin sauri.
Kazalika, a bara, sha’anin masana’antu da sadarwa ya taka rawar gani yayin da ya kai kashi 40% bisa dari na samar da bunkasar tattalin arzikin Sin, kana hakan ya sa ya zama wani babban karfi mai dorewa ga bunkasa tattalin arzikin Sin. (Amina Xu)