• English
  • Business News
Friday, October 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sashen Raya Al’Adu Da Yawon Shakatawa Na Kasar Sin Na Kara Ingiza Bunkasuwar Tattalin Arzikin Kasar

by CMG Hausa
3 years ago
Kasar Sin

A yau Laraba 24 ga watan Agusta, sashen watsa bayanai na JKS, ya gudanar da taron manema labarai, inda a yayin taron aka bayyana cewa, tun bayan taron wakilan JKS karo na 18 da aka gudana yau shekaru 10 da suka gabata, sashen raya al’adu da yawon shakatawa na kasar Sin, ke kara ingiza bunkasuwar tattalin arzikin kasar.

Kaza lika sashen ya zamo sabon karfi dake taka muhimmiyar rawa wajen ingiza sauye-sauye da daga matsayin tattalin arzikin kasar Sin, da kara kyautata nagarta, da biyan bukatun rayuwar al’ummar kasar.

  • Sin Ta Bayyana Kalaman Jakadan Amurka A Sin A Matsayin Shaidar Dake Nuna Tunani Irin Na Danniya

Da yake karin haske game da hakan, babban darakta mai kula da ci gaban masana’antu, a ma’aikatar raya al’adu da yawon shakatawa ta Sin Miao Muyang ya ce, Sin ta kaddamar da sabbin matakai da dama, na bunkasa sashen raya al’adu da yawon shakatawa.

Da farko, fannin masana’antun yana ta kara fadada, kana kasuwar fannin na kara samun tagomashi.

Na biyu, ana kara samun fadadar hidimomin sashen, kuma dunkulewar sassan masana’antun bangaren na ingiza damar cin gajiya daga sashen.

LABARAI MASU NASABA

Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin: Sin Za Ta Kyautata Matakan Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

Na uku, kudaden jari da na hada hadar cinikayya a sashen na karuwa, yayin da ake kara samun manyan nasarori a cinikayyar waje ta fannin.

Na hudu, gwamnati ta ci gaba da fadada matakan tallafawa fannin, ta yadda zai iya kaiwa ga jure mummunan tasirin annobar COVID-19.

A nasa bangare, mataimakin ministan ma’aikatar raya al’adu da yawon shakatawa Rao Quan ya ce, tun bayan taron wakilan JKS karo na 18 da aka gudana yau shekaru 10 da suka gabata, an ga babban tasirin gajiyar da aka samu daga fannin yawon shakatawar yankunan karkarar kasar Sin, wanda shi ma ya zama wani muhimmin bangare na farfadowar yankunan karkarar kasar.

Karkashin wannan nasara, kauyuka kamar su Shibadong na lardin Hunan, da Huamao na yankin Zunyi a lardin Guizhou, sun cimma nasarar kawar da talauci da samun guraben ayyukan yi ta hanyar yawon bude ido.

Bisa wannan nasara ne ma, aka ayyana kauyukan Yucun na lardin Zhejiang, da kauyen Xidi na lardin Anhui, a matsayi na farko a duniya, ta fuskar yawon shakatawa na yankunan karkara, wanda hakan ya zamewa kasar Sin muhimmin abun alfahari da take gabatarwa duniya. (Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin: Sin Za Ta Kyautata Matakan Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth
Daga Birnin Sin

Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin: Sin Za Ta Kyautata Matakan Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth

October 17, 2025
Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika
Daga Birnin Sin

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

October 16, 2025
Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa
Daga Birnin Sin

Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

October 16, 2025
Next Post
Wasu Ayyuka Tara Za Su Bunkasa Ci Gaban Hadin Gwiwar Sin Da Afrika Ta Kowacce Fuska

Wasu Ayyuka Tara Za Su Bunkasa Ci Gaban Hadin Gwiwar Sin Da Afrika Ta Kowacce Fuska

LABARAI MASU NASABA

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta

October 17, 2025
Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin: Sin Za Ta Kyautata Matakan Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth

Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin: Sin Za Ta Kyautata Matakan Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth

October 17, 2025
A Zango Mai Zuwa Za A Fara Aikin Dala Miliyan Daya A Tashar Jirgin Ruwa Ta Legas – Dantsoho

Zan Tabbatar Ana Tafiyar Da Ayyuka A Tashoshin Jiragen Ruwa A Afrika Ta Yamma —Dantsoho

October 17, 2025
Dantawaye Ya Karɓi Ragamar Aiki A Matsayin Sabon Kwamishinan Ƴansandan Abuja

Dantawaye Ya Karɓi Ragamar Aiki A Matsayin Sabon Kwamishinan Ƴansandan Abuja

October 17, 2025
peter

2027: Peter Obi Ya Shiga Rudani Kan Jam’iyyar Da Zai Tsaya Takara

October 17, 2025
Ƙungiyar NNYLF Ta Gargaɗi Atiku Da Sowore Kan Cinna Wutar Rikici A Nijeriya

Ƙungiyar NNYLF Ta Gargaɗi Atiku Da Sowore Kan Cinna Wutar Rikici A Nijeriya

October 17, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilin Karyewar Farashin Kayan Abinci

Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilin Karyewar Farashin Kayan Abinci

October 17, 2025
Tinubu

Batun Yin Afuwa Ga ‘Yan Yankin Ogoni Huɗu

October 17, 2025
Shettima

‘Yan Nijeriya Na Dab Da Fita Daga Halin Kuncin Talauci – Shettima 

October 17, 2025
Manzon Allah

Manzon Allah (SAW) Ne Ya Kafa Tushen Wayewar Kai A Duniya

October 17, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.