Bayanai sun nuna cewa, masana’antar sadarwa ta kasar Sin ta taka rawar gani a cikin watanni 7 na farkon wannan shekara, inda aka samu ci gaba a harkokin kasuwanci masu tasowa da ayyukan 5G.
Ma’aikatar masana’antu da fasahar watsa labaru ta kasar Sin ta bayyana cewa, kamfanonin dake wannan fanni sun samu kudin shiga da ya kai yuan triliyan 1.01 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 140.51 a wannan lokaci, wanda ya karu da kashi 6.2 idan aka kwatanta da daidai lokacin na bara.
Fasahar 5G na ci gaba da samun karbuwa a daidai wannan lokaci, kasar Sin tana da kusan tashoshin 5G miliyan 3.06, ya zuwa karshen watan Yuli,
Bayanai sun tabbatar da cewa, a karshen watan da ya gabata, adadin masu amfani da wayar salula ta 5G tare da manyan kamfanonin sadarwa na kasar guda uku —– China Telecom, China Mobile and China Unicom, ya kai miliyan 695, wanda ya karu da miliyan 134 daga karshen shekarar 2022, wato kashi 40.6 cikin dari na adadin masu amfani da wayar salula. (Yahaya)