Jami’i a ma’aikatar albarkatun kasa ta kasar Sin Gu Wu, ya ce a rabin farko na shekarar bana, sashen tattalin arzikin teku na Sin ya bunkasa bisa daidaito. Gu Wu, ya bayyana hakan ne a Larabar nan, yayin da yake tsokaci a wani zaman tattauna batutuwan tattalin arziki na Sin, wani dandali na kafofin watsa labarai da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ya shirya.
Wasu alkaluman ma’aikatar albarkatun kasa ta Sin, sun nuna yadda mizanin awon albarkatun teku na Sin ko GOP, ya karu da kaso 5.8 bisa dari a mizanin shekara, zuwa darajar yuan tiriliyan 5.1, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 714.1 a rabin farko na shekarar nan ta 2025.
Kazalika, alkaluman sun nuna yadda sashen na tattalin arzikin teku na Sin ya cimma muhimman nasarori a shekarar 2024 da ta gabata, inda mizanin GOP na sashen ya haura tiriliyan 10 a karon farko. Har ila yau, mizanin GOP na Sin ya kai yuan tiriliyan 10.54 a shekarar ta 2024, wanda hakan ya shaida karuwar kaso 5.9 bisa dari kan alkaluman shekarar da ta gabace ta. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp