• English
  • Business News
Friday, October 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Saudiyya Da Iran Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Dawo Da Huldar Jakadanci Tare Da Sake Bude Ofisoshin Jakadanci A Tsakaninsu

by CMG Hausa
3 years ago
Saudiyya

Kamar yadda kasashen Sin da Saudiyya da Iran suka sanar a ranar Jumma’ar da ta gabata, kasashen biyu wato Saudiyya da Iran, sun cimma matsaya, wadda ta hada da yarjejeniyar dawo da huldar jakadanci da ma sake bude ofisoshin jakadanci da sake tura jakadu a tsakaninsu cikin watanni biyu.

Karamin ministan harkokin wajen kasar Saudiyya, kuma mamba a majalisar ministocin kasar, kana mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasar Musaad bin Mohammed Al-Aiban, shi ne ya jagoranci tawagar kasar ta Saudiyya, yayin da sakataren majalisar kolin tsaron kasar Iran, Admiral Ali Shamkhani ya jagoranci tawagar kasar Iran a lokacin tattaunawar da ta gudana a birnin Beijing, fadar mulki kasar Sin daga ranakun 6 zuwa 10 ga watan Maris, kamar yadda wata sanarwar bangarorin uku da suka hada da kasashen Sin, Saudiyya da Iran suka bayyana.

  • Aikin Hajjin 2023: Nijeriya Ta Kulla Yarjejeniyar Fahimtar Juna Da Gwamnatin Saudiyya

Sanarwar ta ce, kasashen Saudiyya da Iran duk sun mika godiyarsu ga kasashen Iraki da Oman, bisa daukar nauyin gudanar da shawarwari da dama tsakanin shekarar 2021 zuwa ta 2022, da kuma shugabanni da gwamnatin kasar Sin da suka dauki nauyin gudanar da shawarwarin, gami da goyon baya da kuma gudummawar da ta kai ga samun nasarar shawarwarin.

Yayin da yake taya bangarorin biyu murnar daukar wani mataki na tarihi, daraktan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin kolin JKS Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin tana goyon bayan bangarorin biyu wajen samun ci gaba mai inganci kamar yadda aka cimma cikin yarjejeniyar, ta yin aiki don samun kyakkyawar makoma tare da yin hakuri da nuna hikima.

Ita ma MDD ta yi maraba da wannan yarjejeniya da kasashen Saudiyya da Iran din suka cimma ta sake farfado da huldar diflomasiyya a wannan rana, kana ta yaba da rawar da kasar Sin ta taka a wannan lamari. Bugu da kari, kasashen Oman, da Türkiye, da Lebanon, da Iraki da sauran kasashe, sun fitar da sanarwa, inda suka yi maraba da sanarwar hadin gwiwa da bangarorin uku suka fitar.

LABARAI MASU NASABA

Ma’aikatar Wajen Sin Ta Yi Tsokaci Kan Amincewar Da Isra’ila Ta Yi Da Yarjejeniyar Kawo Karshen Rikicin Gaza

Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya yi tsokaci kan tattaunawar da aka yi tsakanin kasashen Saudiyya da Iran a nan birnin Beijing, wanda ya samu kulawa sosai daga bangarori daban-daban.

Kakakin ya ce, tare da hadin gwiwar bangarorin da abin ya shafa, tattaunawar da aka yi tsakanin kasashen na Saudiyya da Iran a birnin Beijing, ta haifar da kyakkyawan sakamako. Kasashen Saudiyya da Iran sun fitar da taswira da kuma lokacin da za a bi, wajen kyautata hadin gwiwarsu, wanda ya samar da wani ginshiki mai kyau, na ciyar da hadin gwiwarsu gaba da kuma sake bude wani sabon babi a huldarsu.

Kakakin ya jaddada cewa, kasar Sin ba ta nuna son kai ko kadan a yankin Gabas ta Tsakiya, yana mai cewa, kasar Sin na mutunta matsayin kasashen yankin Gabas ta Tsakiya, kasancewar wannan yanki nasu ne, kuma tana adawa da gasar siyasa a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ya kuma bayyana cewa, kasar Sin ba ta da wata niyya, kuma ba za ta nemi cike wani gurbi ba, ko kuma kafa kungiyoyi na musamman, yana mai cewa, kasar Sin a ko da yaushe tana ganin cewa, ya kamata a ko da yaushe, makomar yankin Gabas ta Tsakiya ta kasance a hannun kasashen yankin. (Ibrahim Yaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ma’aikatar Wajen Sin Ta Yi Tsokaci Kan Amincewar Da Isra’ila Ta Yi Da Yarjejeniyar Kawo Karshen Rikicin Gaza
Daga Birnin Sin

Ma’aikatar Wajen Sin Ta Yi Tsokaci Kan Amincewar Da Isra’ila Ta Yi Da Yarjejeniyar Kawo Karshen Rikicin Gaza

October 10, 2025
Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya
Daga Birnin Sin

Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya

October 10, 2025
CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa
Daga Birnin Sin

CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa

October 10, 2025
Next Post
Manzon Allah

Bita Da Karashen Darasi A Kan Kyawon Cika Alkawari Na Annabi (SAW)

LABARAI MASU NASABA

Ma’aikatar Wajen Sin Ta Yi Tsokaci Kan Amincewar Da Isra’ila Ta Yi Da Yarjejeniyar Kawo Karshen Rikicin Gaza

Ma’aikatar Wajen Sin Ta Yi Tsokaci Kan Amincewar Da Isra’ila Ta Yi Da Yarjejeniyar Kawo Karshen Rikicin Gaza

October 10, 2025
A Zango Mai Zuwa Za A Fara Aikin Dala Miliyan Daya A Tashar Jirgin Ruwa Ta Legas – Dantsoho

Birnin Tarayya Zai Taimaka Da Tara Kudin Shiga Daga Fannin Da Bai Shafi Mai Ba — Dantsoho

October 10, 2025
Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya

Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya

October 10, 2025
peter

Peter Obi Ya Bukaci INEC Ta Tabbatar Da Shaidar Karatun Dan Takara Kafin Shiga Zabe

October 10, 2025
CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa

CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa

October 10, 2025
Jonathan

Maƙiyan Jonathan Ne Kaɗai Za Su Zuga Shi Ya Fito Takara A 2027 – Oshiomhole

October 10, 2025
Sin Za Ta Fara Cajin Kudi Na Musamman Ga Jiragen Ruwan Amurka

Sin Za Ta Fara Cajin Kudi Na Musamman Ga Jiragen Ruwan Amurka

October 10, 2025
Majalisa Na Duba Yiwuwar Amincewa Da Gudanar Da Zaɓen 2027 A Rana Ɗaya

Majalisa Na Duba Yiwuwar Amincewa Da Gudanar Da Zaɓen 2027 A Rana Ɗaya

October 10, 2025
Kasar Sin Ta Samu Manyan Nasarori A Fannin Inganta Walwalar Yara Da Tsoffi Cikin Shekaru 5 Da Suka Gabata  

Kasar Sin Ta Samu Manyan Nasarori A Fannin Inganta Walwalar Yara Da Tsoffi Cikin Shekaru 5 Da Suka Gabata  

October 10, 2025
Tufka Da Warwarar INEC Kan Yiwuwar Zaben 2023

2027: INEC Ta Nemi A Gaggauta Amincewa Da Ƙudirin Sake Fasalin Tsarin Zaɓe

October 10, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.