Yawan Sanatocin Jam’iyyar APC a Majalisar Dokoki ta Kasa ya karu zuwa 76 bayan ficewar dan majalisar da ke wakiltar Kuros Riba ta Arewa, Sanata Jarigbe Agom Jarigbe, daga Jam’iyyar PDP.
Jarigbe, wanda a baya ya sanar da shirinsa na komawa jam’iyyar mai mulki a makon da ya gabata, ya koma APC a hukumance a zaman majalisar na ranar Talata.
- An Kaddamar Da Babbar Hanyar Mota Da Sin Ta Tallafa Wajen Ginawa A Namibia
- ‘Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Kashe Ɗan Wasan Barau FC A Katsina
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, wanda ya jagoranci zaman majalisar ne ya karanta wasikar ficewarsa a yayin zaman.
Da yake bayyana hujjarsa ta ficewa, Sanata Jarigbe ya ambaci “rabuwar kawuna a cikin PDP” a matsayin dalilin barin babbar jam’iyyar adawar.
Da ficewarsa, PDP yanzu tana da kujeru 25 a Majalisar Dattawa, yayin da Jam’iyyar Labour ke da 4, APGA tana da 2, SDP tana da 1, sai kuma NNPP da ke da 1, wanda hakan ya kawo jimillar Sanatocin zuwa 109.
ADVERTISEMENT














