Bankin Zenith ya rufe wasu rassansa da ke babban birnin tarayya Abuja da wasu jihohin kasar nan sakamakon hare-haren da ake kai wa wasu rassansa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) wanda ya sanya ido a kan wasu rassan bankin a FCT da kewaye da wasu jihohi a ranar Talata, ya gano cewa an kulle wasu rassa.
A reshen bankin Zenith da ke kan titin Nyanya Mararaba, kofar shiga bankin da dakin ATM na bankin duk a kulle suke, babu kwastama a wajen.
Wani jami’in bankin da ya so a sakaya sunansa ya bayyana cewa an kuma rufe wasu rassan bankin ne sabida rashin sabbin takardun kudi a bankin.
Jami’in ya bayyana cewa kwastomominsu ne suka kai wa da yawa daga cikin rassansu da ke fadin kasar nan hari wadanda suka kasa cire sabbin takardun kudin daga asusunsu.