Dan takarar jam’iyyar SDP Ahmed Wadada, ya lashe zaben Sanatan Nasarawa ta Kudu a zaben da aka kammala a jihar Nasarawa.
Nasarawa ta Kudu ita ce gundumar sanata na shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta kasa, Sanata Abdullahi Adamu, kuma shi ne Sanata a kujerar kafin mukamin da yake yanzu.
Wadada ya samu kuri’u 96,488 inda ya doke dan takarar jam’iyyar APC, Injiniya Ahmed Tukur, ya zama Sanatan mazabar Nasarawa ta kudu a sakamakon zaben da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana a safiyar ranar Litinin.
Sakamakon zaben dai ya nuna cewa babbar jam’iyyar adawa ta PDP da Labour Party (LP) ta samu kuri’u 46,820 da kuri’u 23,228.
Haka kuma, an ayyana Sanata Godiya Akwashiki na SDP a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar Asabar na mazabar Nasarawa ta Arewa.
Jami’in zaben na INEC Farfesa Ilemona Adofu na Jami’ar Tarayya da ke Lafiya a safiyar ranar Litinin a Akwanga ya bayyana Akwashiki a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 44,471.
Akwashiki ya doke Alhaji Danladi Halilu na jam’iyyar APC, wanda ya samu kuri’u 32,058.
Jam’iyyar SDP dai ta lashe mazabar Karu/Keffi/Kokona na jihar a zaben yayin da Jonathan Gaza ya sake lashe zaben kujerar sa a majalisar wakilai.