Asusun kula da raya kasa da zuba jari na kasar Senegal FONSIS, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa da kamfanin Sinohydro na kasar Sin, domin gudanar da wani katafaren aikin karkatar da ruwa.
Bisa yarjejeniyar da aka rattabawa hannu ranar Alhamis, kamfanin Sinohydro zai gina hanyar ruwa mai tsawon km 250 domin jigilar ruwa daga tabkin Guiers dake arewacin Senegal zuwa yankunan Mbour zuwa Dakar zuwa Thies dake yammacin kasar, wadanda mazauni ne ga adadi mai yawa na al’ummar kasar.
- EU Za Ta Janyowa Kan Ta Lahani Sakamakon Kakaba Karin Haraji Kan Motoci Masu Aiki Da Lantarki Kirar Sin
- Jihohin Da Suka Amince Su Fara Biyan Mafi Ƙarancin Albashin Ma’aikata
Ana sa ran kammala aikin wanda asusun FONSIS zai samar da kudin aiwatarwa a shekarar 2028.
Darakta janar na asusun FONSIS Babacar Gning, ya ce an zabi kamfanin Sinohydro ne saboda farashi mai kyau da ya gabatar da kudurinsa na aiwatar da aikin cikin sauri da kuma amfani da ma’aikata ‘yan asalin wurin, idan Senegal ta amince tsarin gudanar da aikin.
Minisitan kula da harkokin ruwa da tsafta na kasar Senegal, Cheikh Tidiane Dieye ya ce kamfanin Sinohydro ne kadai ya cika dukkan sharuddan da hukumomin Senegal suka gindaya. (Fa’iza Mustapha)