A kwanan nan, shugaban kasar Italiya Sergio Mattarella, ya gudanar da ziyara karo na biyu a kasar Sin a wa’adin aikinsa, inda kuma wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ta samu damar tattaunawa da shi.
A lokacin ziyararsa a kasar Sin, Mattarella ya halarci wasu ayyuka da dama na yin musayar al’adu tsakanin kasar Sin da Italiya. A tattaunawarsa da wakilin CMG, yayin da yake tsokaci kan shawarar wayewar kan duniya da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, ya ce bude kasuwanni, da mu’amalar cinikayya, za su samar da yanayin da zai yi amfani ga juna, da samun nasara tare, matakan da suka kasance ‘maganin’ yin fito na fito da yaki da juna, da kuma inganta jin dadin jama’a. Don haka, duk matakan da ke rungumar hadin gwiwa, da mu’amalar tattalin arziki da cinikayya, ko musayar al’adu, dukiyoyi ne masu kima na kasashen duniya baki daya.
(Mai fassara: Bilkisu Xin)