Shafin Taskira, shafi ne daya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da zamantakewar Aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu. Tsokacinmu na yau zai yi duba game da shagulgulan sallah da a ke ciki, duba da yadda wannan sallar ta zo cikin yanayi na rashin kudi, dalilin hakan ya sa wannan shafi jin ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin Taskira game da wannan batu; Ko wane tanadi aka yi wa wannan sallar?, A kowacce shekara akan fidda sabon salon shigar kaya ko wasu abubuwan na daban, ko a wannan sallar an fidda wani sabon kalar ankon?
Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Rahma Ahmad, Daga Jihar Kano:
Mu dai mun yi wa sallah tanadi da dama saboda kowa jira yake ya ga ya fi wancan, amma tanadin ba zai zama kamar na bara ba da kuma sauran shekarun da suka wuce domin yanayi ne na tsadar rayuwa. A gaskiya ban sani ba, ni a nawa ganin ma ba za a yi yayi ba saboda kowa abun da Allah ya hore masa zai saka, sai dai hijab dana gani yana yaho. Ni dai ina son cin abubuwa da yawa kamar su; Wainar shinkafa, Snasir, Dabgen Kaji, Lemon Zobo me dadin gaske, kayan marmari da kuma Snacks. Kayan da nake son sanyawa idan zan je idi sune; Doguwar rigar lace, da sarkar wuya da awarwaro, takalmi mai tsini (mai tudu) da kuma mayafi mai kyau. A ranar sallah akwai ‘kananun yara da matasa da idan sallah tayi za su fara shagulgulan sallah da buga binduga da wasa da mashin da mota a kan titina, alhalin za su iya cutar da wani ta dalilin yin hakan musamman kananan yara, toh dan Allah su canja wasannin akwai wasanni da dama da zas u nishadantar da al’umma.
Sunana Muhammad Kabir Kamji (Dr Muhammad), Daga Batsari A Jihar Katsina:
Tanadin da nayi wa sallah shi ne kamar dai duk shekara abin da aka saba yi sai dai ita wannan sallar ta sha bamban da kowacce duba da matsin rayuwar da ake ciki. Gaskiya bana ce ga abin da za a yi yayinsa ba, amman dai na san wannan shekarar za a yi yayin yadi da shadda, amman inada yakinin cewa yadi zai fi yawa. Gaskiya na fi son shinkafa da miya da dan nama a ciki, sai kunun aya mai sanyi sosai, shi ne abin da na fi so ga sallah. Shawarar da zan ba matasa ita ce su bi komai a hankali kuma su kasance masu tsoron Allah akan duk abin da suka saka a gaba. Kuma su yi hakuri da shaye-shayen da ake yi na sallah, sannan su yi hattara da guje-gujen da ake yi da abin hawa ranar sallah. Allah ya sa mu yi sallah lafiya amin.
Sunana Zainab Zeey Ilyas, Jihar Kaduna:
Ai wannan sallar sai dai kawai a yi shuru, amma ba kamar baya ba, koda ace wani yanada shi to wasu da yawa ba su da shi, ta yu ni ban da damuwa amma wasu da yawa sunada damuwa, ko ni inada damuwa wasu kuma babu, to kamar haka ne. Ni dai anan ban ga yayin da aka fitar ba, kodan ban yi yaho sosai ba ne, amma dai ban ga ni ba, rayuwa tayi tsada. Abincin da nake son ci da zarar na dawo daga sallar idi shi ne Tuwon shinkafa, miyar Agushi ta ji manshanu da kuma naman kaji, sai lemo me sanyi haka ma ya wadatar, kayan da zan saka kuma in zan je sallar idi na tanadi shadda dan zuwa wajen kawai na tanada maroon color ce, sai aka yi mata aikin beat work, amma milk color, da mayafina kalar aikin da aka yi, yayi kyau sosai sai wanda ma ya gani. Shawarata ga matasa kar a yi wasan da bai dace ba, kuma a kula sosai kar a wuce gona da iri wajen kula ‘yan mata da wasu wasannin.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Jihar Kano, Rano:
Gaskiya wannan sallar ta bana ba wani tanadi a ka yi mata kamar na shekarun baya ba, wannan babban tanadin da a ka yi mata bai wuce na ta zo mana cikin koshin lafiya ba, sai kuma dan abin da ba a rasa ba.To manyan mutane dai ba wani yayi sai idan ko yara sai kuma matasa da suke yayin dinka danyar shadda wanda yake bana kuma a namu yankin ba zai wuce yayin dinka yadi ba, shi ma ga wanda ya sami sarari. Ana son cin abinci mai gina jiki kuma mai dan ruwa-ruwa sannan ba a son cin abinci mai zafi sabida azmin da a ka yi. Ana son saka sabon kayan da ba a taba sakawa ba ma’ana dai sabon dinki idan kuma babu ana so a saka kayan da a ka fi ji da shi. Shawarata a nan ita ce; don Allah mu yi shagulgulan sallah cikin hankali da nutsuwa duba da yadda addininmu ya tanada, Allah kasa mudace amin.
Sunana Aminu Adamu, Malam Maduri A Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya yanayin da a ka samu kai a ciki ya sa al’umma da dama babu wani tanadi da suka yi wa bikin sallah, kawai fatan mu a nan shi ne Allah ya nuna mana sallah lafiya shi ma babban arziki ne, kuma muna fatan Allah ya kawo karshen wannan matsala ta tsadar rayuwa da ma tsananin talauci daya addabi al’umma. To magana ta gaskiya wannan sallah ba wai maganar yayi ake ba, ana maganar abun da ya samu ne a yi amfani da shi, domin da yawan al’umma kokari suke su fi karfin abinci ba wai sutura ba a halin da a ke ciki, sai dai kawai addu’ar Allah ya kawo mafita. Duk wadanan ka’idoji ana amfani da sune idan da wadata, amma a halin da ake ciki duk wanda ya samu da shi za a yi amfani, abu mafi muhimmanci a wannan lokaci shi ne addu’o’i da kuma ziyara domin sada zumunci a tsakanin ‘yan uwa da abokan arziki. To shawara a nan ita ce; matasa abu komai a hankali kuma kowa yayi amfani da abun da ya ke da shi wajen yin shagalin sallah ba tare da an takurawa kai ba domin komai yana da lokaci, kuma ya kamata a kiyaye kada a yi wasan ganganci ababen hawa, sai kuma dage kabarori da addu’oin Allah ya kawo mana mafita daga wannan matsala ta tsadar rayuwa dama tsananin talauci, Ameen ya rabbi.
Sunana Hafsat Sa’eed, Jihar Neja:
Ni dai a nan bangarena da nake ban ga alamun an fitar da wani yayi da za a yi a wannan sallar ba, sakamakon yadda kowa yake neman abin da za a ci, gaskiya bana tunanin an fitar da wani yayi na kaya ko wani abu da za a yi a wannan sallar ba. Na ga dai akwai wani hijabai daya fito ya fi trending irin wanda dai ake dinkawa. Toh! Abincin sallah dai sai lokaci ya yi wanda aka samu duk shi ma zai shiga ciki, sai kuma shawarwarin da zan bayar a nan ga masu yin shagulgulan sallah, su yi a hankali, dan ni a nan ma ba ni da wani shiri dana yi wa sallar, sabida ta kai ake yi, ba ta kaya ba.
Sunana Ibrahim Umar Biraji, Malam Madori A Jihar Jigawa:
Wata sabuwa ana babbakar Giwa waye zai jiyo wani ‘kaurin babbakar Sauro, yanzu fa batu ake na abun da za a ri’ka kaiwa baki. Ai a yanayin da muke a ciki ynazu ba na tunanin har za a iya zatawa mutane batun wai shirye-shiryen Sallah. Kawai dai muna jiranta ne ta zo, amma batun shirye-shiryen ta kam bana ce komai ba Sai dai Allah ya bamu dacewa. Eh tabbas kowacce Sallah akwai kalar sabon yayin data ke zuwa da shi, amma bana tunanin wannan ko ta zo da sabon kalar yayin ma, zai samu karbuwa a gurin Al’ummah. Duba da mawuyacin halin da Al’ummar ta tsinci kanta a ciki. A halin da ake ciki yanzu, dai-daikune cikin Al’ummar mu suke amfani da abun da bai zamto wajibi ne shi ba a rayuwa. A zamanin baya kadan daya gabata a iya samun damar yi wa mutane irin wadannan tambayoyin, amma a halin da muke ciki a yanzu bana tunanin mutane suna da irin wadannan ka’idojin, kai koda ma sunada shi to dole ta sa, sai wasu sun yi hakuri da binsu duba da yanayin yadda rayuwa ta sauya cikin kankanin lokaci. Eh! shawarata a nan ga matasa shi ne mu ji tsoron Allah, mu kuma zamto masu yin biyayya wa dukkanin abun da Allah SWT ya yi wa dukkanin musulmin duniya umarni a kansa. Mu dage da yin Ibada yadda ya kamata don ganin mun kaucewa kasantuwa a bisa tafarkin banza, dan ta wannan hanyar ne kawai nake ganin za mu samu sassauci dangane da wannan halin da muka tsinci kan mu a yau.
Sunana Khadija Muhammad, Jihar Kano:
Gaskiya wannan sallar ban yi mata tanadin komai ba, saboda ina makaranta. Nafi tunanin yayin Hijab za a yi, an fi son cin shinkafa da miya da nama kuma zan saka sabon kaya. Shawarar da zan bayar shi ne matasa su kiyaye ban da hawa doki da sauransu.