• English
  • Business News
Thursday, October 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shakku A Kan INEC A Zaɓukan 2023: Ana Taƙaddama Game Da Kashi 94 Cikin 100 Na Kujerun Da Aka Lashe

by Sulaiman
2 years ago
Inec

Sakamakon zabukan da ya gabata da kuma kararrakin zabe da aka shigar a gaban kotu da ba a taba yin irinsa ba, ya kara sanya shakku ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) kan gudanar da sahihin zabe na gaskiya da adalci.

Ko da yake dama, tun dawo da mulki ga gwamnatin farar hula a shekarar 1999, ake shiga kotu kan kararrakin zabe, amma a zaben bana, duba da adadin kararrakin zabe da ke gaban kotun daukaka kararrakin zabe, lamarin na da ban tsoro.

  • Kotun Zaben Gwamnan Taraba: Cikin Matsi INEC Ta Ayyana Sakamako, A Sake Bitar Zaben – NNPP
  • Za Mu Dasa Wa ‘Yan Nijeriya Dabi’ar Gaskata Kalaman Shugabanni A Zukatansu – Minista

A zaben bana, 2023, an gudanar da zabe a kujerun siyasa daban-daban har 1,280 tun daga kan kujerar shugaban kasa, ‘yan majalisar dattijai 109, majalisar wakilai ta tarayya 360, kujeru 782 na majalisar wakilai a fadin jihohi 28 da kuma kujerun gwamnoni 28.

Cikin jimillar adadin, an shigar da kararraki 1,209 a gaban alkalai domin yanke hukunci, kamar yadda shugabar kotun daukaka kara (PCA), Mai shari’a Monica Dongban-mensem ta bayyana a lokacin bikin fara shekarar shari’a ta 2023/2024 a Abuja. Wannan ya nuna cewa, kashi 94.453 cikin 100 na kujerun da aka fafata, suna gaban alkalai.

Kujeru 71 ne kacal cikin 1,280 da aka fafata a zaben ba a garzaya kotu ba. Ya nuna kashi 5.547 cikin 100 kenan.

LABARAI MASU NASABA

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC

Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC

A watan Nuwamban da ya gabata, shugaban hukumar INEC, Mahmood Yakubu, ya koka kan yadda shari’o’i sama da 600 suke gaban hukumar gabanin zabe a kotuna da dama a fadin tarayyar Nijeriya, kamar yadda jaridar the guardian ta rahoto.

Mahmood ya bayyana hakan ne a yayin wani taron karawa juna sani ga alkalai sama da 300 da za su gudanar da shari’o’i kan rikicin zabe.

Ya bayyana cewa shari’o’in da ke gaban hukumar zaben sun shafi yadda jam’iyyun siyasa ke gudanar da zaben fidda gwani, yanzun da aka kammala zabe, shari’o’in sun taso, yanzun INEC za ta yi shari’a kusan 1,209, tunda yawanci masu shigar da kara, sun shigar da INEC a cikin kokensu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sabbin Ministoci
Manyan Labarai

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC

October 16, 2025
Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC
Manyan Labarai

Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC

October 16, 2025
Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC
Manyan Labarai

Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC

October 16, 2025
Next Post
Tinubu Ya Kaddamar Da Shirin Raba Naira Tiriliyan N1.25 Ga Magidanta Miliyan 15

Tinubu Ya Kaddamar Da Shirin Raba Naira Tiriliyan N1.25 Ga Magidanta Miliyan 15

LABARAI MASU NASABA

Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona

Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona

October 16, 2025
Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

October 16, 2025
Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba Wa Sin Kan Gudummawar Da Ta Bayar A Fannin Tabbatar Da Daidaiton Jinsi

Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba Wa Sin Kan Gudummawar Da Ta Bayar A Fannin Tabbatar Da Daidaiton Jinsi

October 16, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC

October 16, 2025
Ɗaga Matsayin Dangantakar Zambia Da Sin Ya Haifar Da Manyan Nasarori

Ɗaga Matsayin Dangantakar Zambia Da Sin Ya Haifar Da Manyan Nasarori

October 16, 2025
Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zaman Kurkuku

Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zaman Kurkuku

October 16, 2025
Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC

Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC

October 16, 2025
Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC

Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC

October 16, 2025
An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

October 16, 2025
Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu

Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu

October 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.