An gudanar da taron majalisar tattalin arziki da zamantakewar al’umma ta kasar Sin da ta nahiyar Afirka da sauran kungiyoyin da abin ya shafa karo na hudu a birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin jiya Jumma’a, inda wakilai kusan 60 daga Sin da Afirka suka yi mu’amala da juna kan yadda za a yi hadin gwiwa don samun moriyar juna da kuma sa kaimi ga zamanintar da Sin da Afirka tare. Mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin kuma babban sakataren majalisar kana shugaban majalisar tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Sin Wang Dongfeng ya halarci taron tare da ba da jawabi.
A cikin jawabinsa, Wang Dongfeng ya bayyana cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da manyan shawarwari shida da ayyukan raya abokantaka guda 10 kan yadda Sin da Afirka za su yi hadin gwiwar zamanintar da kansu a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC, hakan ya nuna taswirar neman cimma burin zamanintar da Sin da Afirka, da kuma raya makomar bai daya ta Sin da Afirka a sabon zamani. Ya kamata majalisar tattalin arziki da zamantakewar al’umma ta kasar Sin da ta nahiyar Afirka su kara yin hadin gwiwa da mu’amala da juna don sa kaimi ga raya shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya mai inganci, da aiwatar da ayyukan da aka cimma daidaito a gun taron koli na Beijing na dandalin FOCAC, da kyautata tsarin majalisar don samar da gudummawa ga sha’anin zamanintar da Sin da Afirka baki daya. (Zainab Zhang)