An fitar da wani sabon tsarin aiki na Shanghai na gina wani yanki da zai zamo kan gaba a fagen tafiyar da motoci masu tuka kansu jiya Asabar, yayin da ake ci gaba da gudanar da taron fasahar kirkirarriyar basira na duniya a birnin dake kudancin kasar Sin.
An tsara shirin ne da nufin ganin motoci masu tuka kansu a mataki na 4 sun yi jigilar fasinjoji fiye da miliyan shida nan da shekarar 2027, tare da bude hanyoyi sama da kilomita 5,000 domin motocin masu tuka kansu, tare da tabbatar da cewa an sanya wa fiye da kashi 90 cikin dari na sabbin motocin birnin na’urorin tuka kai na mataki na 2 da kuma mataki na 3.
An rarraba matakan tuka kai daga mataki na 0 zuwa mataki na 5. Yanayin girman kowane mataki ne yake nuna yanayin fasaharsa. Motoci masu tuka kansu na mataki na 4 na iya tuka kansu a mafi yawan yanayoyi ba tare da an tanadi wani direban ko-ta-kwana ba.
Darektan sashen ba da bayanai na hukumar kula da tattalin arziki da masana’antar kera motoci ta birnin Shanghai Han Dadong, ya bayyana cewa, Shanghai zai hanzarta gina wani yanki da zai zamo kan gaba a duniya wajen tukin motoci masu sarrafa kansu, ta hanyar hadin gwiwar bangarori daban-daban da suka hada da dandalolin tattara bayanai, da sansanonin horaswa, da na manyan tsare-tsaren fasahohin zamani da manufofi. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp