Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da irin Matan da ba sa hakuri da bukatun cikin gida da mazajensu suka saba yi musu a baya, musamman ta yadda rayuwa ta yi tsada a yanzu, a takaice dai rashin godiyar Allah.
Da yawan wasu Matan na da laifi, yayin da wani bangaren kuma Mazan ne ke da laifi, duba da yadda zamani ya sauya. Da yawan wasu Matan na la’akari ne da yadda mazajen suka saba wadatasu ba tare da an samu sauyi ko kankani ba, har sai lokacin da rayuwa ta sauya gaba daya, wasu kuma tsarin auren ne ya zo musu a haka ta yadda namijin ya nuna fafa da karya ba tare da nuna ainihin gaskiyarsa ba, har sai da rayuwa ta sauya masa gaba daya.
- Yanzu-Yanzu Tinubu Na Ganawa Da Kwakwaso
- Masana Da Jami’an Kasashen Sin Da Tanzania Sun Sha Alwashin Inganta Hadin Gwiwa Tsakanin Kasashe Masu Tasowa
Wasu Matan kuma rashin fahimtar juna ne da babu tun a farkon haduwa ko kuma farkon aure da rashin fayyacewa mace samu da rashinsa kamar dai yadda na yi bayani a baya kullum cikin fafa, wani kuma ra’ayinsa ne a haka baya bukatar sanarwa mace yana da shi ko ba shi da shi. Wasu matan kuma hange-hange ne na kawaye ko makwafta ko ‘yan uwa, na rashin tsayawa a matsayin da Allah ya ajjiye su na sun fi wani ko da kuwa wasu sun fi su, su a lallai sai sun kai kansu in da Allah bai kaisu ba, ta masu iya magana kan ce; ‘In ba ka da gashin wane – kar ka ce za ka yi kitson wance’, tofah! su sai sun yi ko da mijin ba shi da shi sai an tilasta masa ya yi, kullum cikin rigima da tashin hankali da rashin jituwa da rashin zaman lafiya da tonan asiri miji ba shi da shi ko ya ki yi. Yayin da wani bangaren kuma namijin ne ke janyo hakan, duk da cewa ba shi da shi amma yana iya kashe wa ‘Yan Mata na waje kudi ko da kuwa zai ciwo bashi ne, ba zai taba nuna musu ba shi da shi ba, amma ‘ya’yansa da Matansa sai dai su kwana da yunwa ko kuma su ci bai ishe su ba, ba zai taba nuna cewa yana da shi ba, ko ya samu, a duk lokacin daya samu kudi burinsa ya kashewa ‘Yan Mata, kullum yana cikin babu har sai ranar da matar ta gano gaskiyar lamari anan bom din zai fashe, wannan a takaice kenan. Akwai dalilai da dama da ke jawo hakan wanda wajen yayi kadan na zayyane muku shi, musamman ta yadda zan baje muku ra’ayoyin mabiya shafin Taskira, “Ko me yake jaho hakan da har Matan ba sa iya yi wa Mazan Uzuri?, Shin laifin Matan ne ko na Mazan?, Wacce shawara za a ba wa masu irin wannan halin?”, Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka:
Fadila Lamido daga Jihar Kaduna:
Duk macen da za ta kasa hakuri da wani bukata da aka saba yi ma ta a baya, yanzun kuma ya gagara rashin fahimta ne a tsakaninsu da mijin wadda a cikin biyu za a samu daya, ko dai daman can macen ta aure shi ne domin abin hannun shi, ko kuma shi mijin yana da wani yanayi na nuku-nuku wadda har zai sa ta kasa yadda da yanayin da yake ciki a yanzun, idan ya zama cewa domin abun hannunsa ta aure shi, dole idan ba ta samun yadda take so ba ta kasa hakuri, haka kuma ko da ace domin Allah take aurensa idan ya kasance shi mijin ya kasance me nuku nuku ne baya bude ma ta komai Mace na iya ta da rigima ko da ace da gasken bai da shi, ba za ta yadda da shi ba. Saboda wannan nuku-nukun da yake baya fitowa ya fayyace ma ta komai, a tunani na idan Mace na son mijinta domin Allah, kuma suna da fahimta me kyau a tsakaninsu, ba za ta ta da hankali da yanayin rashin da ya samu daga baya ba, domin mace da tausayi aka santa, kuma ita ganauce ba jiyau ba, a baya yana yi, yanzun da babu sai dai tausayawa ya biyo baya ba rigima ba. Shawarata ga masu fuskantar irin wannan matsalar musamman ga shi Namijin, yana da kyau kwarai ya rinka bude ma ta komai, idan yau akwai ta san akwai, idan kuma ka ce babun ya zama babun ne da gaske har ga Allah, kar ka ce ma ta babu ta kuma kama ka da yi ma ta karya, domin zargin a kwai ake cewa babu – shi ke sa Mace ta kasa yi wa mijinta uzuri har a lokacin da bai da shi din da gaske. Dan haka a gina auren gaba dayan shi akan gaskiya da amana.
Binta Dalha Usman daga Jihar Kano:
A gaskiya matan da ba sa iya hakuri da abin da mazajensu suke yi musu ‘ada’, yanzu rashin tawakkali ne da rashin hakuri saboda yanzu kowa ya san yadda rayuwa take. Abin da yake janyo hakan shi ne; mazan sun riga sun saba musu da ko da yaushe asha rayuwa ba sa nuna musu cewar a rinka hakuri wata rana fa za a iya tsintar kai a halin babu saboda rayuwa ta canza. Mazan ba suda laifi sosai matan sun fi laifi saboda ya kamata su san cewa; yau da gobe sai Allah wataran zuma watarana madaci, ba zai yi wu ace kullum aji dadi ba dole Allah ya jarrabi mutum in dai yana raye. Shawarata a gare su ita ce su yi hakuri da duk halin da suka tsinci kansu a rayuwa kar mace ta zama butulu idan mijinki ya kawo mai dadi ki karba ki ci idan sabanin hakane ma ki karba ki yi Masa addu’a, Allah ya sa masa albarka ya kara budi, a haka shi ma zai ji dadi ko da bai samo ba ya san Allah ya bashi mace ta gari.
Aminu Bello Muhd Kano:
Mafi yawanci hakan ya samo asali tun daga tarbiyyar da aka bata a gidansu wanda shi ake kira da ‘wadatar zuci’, a matsayinka na mijinta sai kayi kokarin gyara ma ta wannan halin. Abin da ke janyo matan ba sa iya yi wa mazan uzuri shi ne rashin tarbiyya ko kuma hucubar kawaye da hangen cewa wata mijinta ya yi ma ta abu sai ita ma ta matsawa na ta cewa; sai ya yi mata. Gaskiya mata suna da kaso mafi tsoka a cikin laifin hakan, amma maza su ji tsoron Allah su kyautatawa matayensu. Shawarata ga mataye masu aikata hakan su tuba su daina domin ba abu ne mai kyau ba.
Yusif (Boso) Jihar Kano:
Gaskiya hakan na ci mini tuwo a kwarya duba da cewa hakan na haifar da matsala ga ma’aurata har ta kai ga sakin aure. Kar su manta cewa abubuwa yanzu sun canza kuma rayuwa sai a hankali. Abin da ke jawo hakan rashin tarbiyya da aiki da ilimin da mutum ke da shi, Gaskiya laifi ne ga kowanne bangare, fatan mu dai a gyara. Shawarata anan shi ne; Maza su ji tsaron Allah su kuma Mata su tausayawa mazajensu su tuna cewa babu wata wahala da tsanani da za su dawwama.
Hafsatu Yusuf Muhammad daga Jihar Kano:
Abin da zan cewa matan da basa iya hakuri da bukatun da mazajensu suka saba yi musu a baya yanzu kuma ba sa samu shi ne; Su yi hakuri domin a baya ya yi miki, yanzu kuma dan babu ai sai ku hadu ku rufawa kai asiri, shi ma ba a san ransa bane hakan jarabawace ta ubangiji, sai a rinka yi masa addu’a, Allah ya hore ya kuma buda duniya da lahira. In kika yi hakan wallahi zai ji dadi sosai, da za ki duba zuciyarsa wallahi shi ma baya jin dadin rashin yi miki abin da ya saba, domin kowa yana so ya ga ya ci gaba duniya da kuma lahira, Allah ya sa mu dace Ameen. Abin da yasa wasu matan ba sa yi wa wasu mazan uzuri sabida wani dama ya saba ko yana dashi baya basu wanda zai Isa ba za ta gane samunsa ba, kuma ba za ta gane rashin samunsa ba, wata matar ita ba ta san babu ba, kawai ko sata zai yi sai ya samo ya bata ba ruwanta. Gaskiya babu wanda ba shi da laifi, amma na mijin ya fi tunda ya san shi ne mai kawo wa dole shiyasa ake samun matsala da kuma rashin hakuri, Allah yasa mana hakuri a cikin zuciyar mu. Shawarar da zan bawa masu irin wannan su rinka hakuri da biyayya tunda zama ne ba na karewa ba na ibada, Allah ne ya san irin ladan zaman gidan aure, Allah ya bamu hakuri da juriya, Amin.
Maryam Rabi’u Musa daga Jihar Kano:
Ya kamata ace mata su gane yadda aka shiga cikin wani hali, na tsadar kayan masarufi, su yi hakuri da abin da mazajansu za su basu ko mai kankantar sa, duba da rayuwarce ta canja sabanin ta da. Rashin hakuri ne ke janyo hakan, da yawa dai laifin mata ne, tunda suma mazan ba haka suka so ba. Shawara dai ita ce; su yi hakuri da halin da suka tsinci kansu a ciki.
Musa Rabi’u Ali Gama-C Jihar Kano:
Ni a ganina in dai har mace ta yarda cewa ta auri namiji saboda Allah kuma dan ibada to ya kamata ta iya hakuri da duk yanayin da ya tsinci kansa na akwai da babu, shi aure ai mutunci da girmamawa shi ne aure. Abin da yake janyo hakan akwai hangen da wasu suke yi wa wadanda suke sama da su wajen wadata, suna ganin su rashin wadatar aurensu su naka su ne yasa suke tayarwa da mazajensu hankali rashin tawakkali. Laifin matan ne, shawarar da zan basu shi ne; su tuna cewar lokacin da yake dashi ba dabarar sa ce ta basa ba yanzu ma da ya rasa ba rashin kokarinsa bane samu da rashi daga Allah suke dogaro da Allah kuma jari.
Fauziyya Madaki Jihar Kaduna:
Jan hankali ga masu irin halayen nan tun kafin lokaci ya kure miki ki yi karatun ta nutsu, ki gyara halinki tun kafin mijinki ya gaji da halayenki ki bashi hakuri ku zauna lafiya, idan Allah ya hore masa sai ki ga ya ninka abin da yake yi miki a baya. Dalilai masu yawa suna janyo hakan, rashin sanin darajar aure, da rashin sanin darajar mijin, rashin tawakkali, a wasu lokutan ma rashin tausayi yana janyo hakan. Kaso 80 cikin 100 yana kasancewa laifin matan ne, domin mata da yawa ba ruwansu da ya samun mijinsu yake su dai kawai a yi musu abin da ransu yake so a lokacin da suka so. Shawara ga ‘yan uwa mata masu irin wannan halin ku canza hali, tun kafin zuwan ranar nadama ko zubewar mutunci a idon miji da danginsa, kiyi hakuri ku zauna lafiya, da dadi ba dadi ki ci gaba da hakuri, Allah yana tare da masu hakuri.