Jama’a, ko kun sha karanta rahotanni da ke cewa, wai “Jarin da kasar Sin ke zubawa Nijeriya suna haifar da matsalar bashi a kasar”, ko “Hadin gwiwa da ke tsakanin Sin da Afirka sabon salon mulkin mallaka ne da kasar Sin ta aiwatar a Afirka”, ko “Bunkasuwar kasar Sin barazana ce ga duniya”? Bayan kun karanta, ko ku ma kuna kallon kasar Sin a matsayin mummunar kasa, har ma kun fara nuna shakku kan hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka? Idan abin haka yake, lallai, ya kamata ku yi hankali, sabo da rahotannin ka iya zama na jabu, wadanda ake samarwa karkashin wani shirin doka da ya shafi dala biliyan 1.5.
Kwanan nan, Jan Oberg manazarci a wani asusun nazari na kasar Sweden da ake kira Transnational Foundation for Peace and Future Research, ya fayyace cewa, majalisar dokokin kasar Amurka ta zartas da wani shirin doka a kamanin shekaru 5 da suka wuce, wanda ya yi shirin biyan dala biliyan 1.5 cikin shekaru biyar, a yunkurin horar da ‘yan jarida na kasashen yamma wajen rubuta rahotannin neman shafa wa kasar Sin kashin kaza. Dala biliyan 1.5, ba wani abin mamaki ba ne, ganin yadda kafofin yada labarai na kasashen yamma suka yi ta shafa wa kasar Sin kashin kaza a cikin ‘yan shekarun baya.
- Babban Jami’in Diplomasiyyar Sin Ya Takaita Abubuwan Da Hadin Gwiwar Sin Da Amurka Ya Kawo
- Adadin Kudin Musaya Da Sin Ta Adana Ya Kai Dala Biliyan 3238 A Karshen Bara
Ban da haka, gwamnatin Amurka ta kuma yi ta zuba makudan kudade a kasashen ketare, don sayen kungiyoyin da ba na gwamnati ba da ma ‘yan jarida na kasashen, da su rika bata sunan kamfanonin kasar Sin da ma ayyukan da suka gudanar. Misali, a shekarar 2021, jaridar The Herald ta kasar Zimbabwe ta ba da labarin cewa, Amurka ta yi amfani da ofishin jakadancinta dake kasar wajen samar da kudade ga wasu cibiyoyi, domin shirya tarukan karawa juna sani, da sayen rahotannin kafafen watsa labarai masu zaman kan su, kan kudi har dalar Amurka 1000 kan ko wacce makala, inda ake umartar su da su rubuta rahotani suna sukar jarin da kamfanonin Sin ke zubawa a Zimbabwe.
Rashin kunya ne yadda Amurka ta dauki irin wadannan munanan matakai, amma kuma ya kamata mu yi hankali da manufar da take neman cimmawa. Dalilin da ya sa Amurka ke zuba kudade tana sayen ‘yan jarida shi ne, tana bukatar kafofin yada labarai su taimaka mata wajen cimma burinta, ko wajen neman tsoma baki a harkokin wasu ko kuma don wanke kanta daga laifuffukan da ta aikata. Misali a shekarar 2003, kafofin watsa labarai da dama sun yi ta watsa rahotanni wai “Iraki ta mallaki makaman kare dangi”, wanda hakan ya zamawa Amurka wani dalilin ta da yaki. Sai dai binciken da aka gudanar bayan yakin ya shaida cewa, sam babu irin wadannan makamai a kasar ta Iraki, wato rahotannin karya ne.
A yayin da kasar Sin ke dada bunkasa, ita Amurka ta yi kuskure har ta dauki kasar Sin a matsayin babbar abokiyar takarar ta ta farko, lamarin da ya sa ta dauki matakai na dakile kasar Sin daga dukkan fannoni, ciki har da fannin yada labarai. Daga wanke masu tada zaune tsaye a yankin Hongkong daga laifin da suka aikata, zuwa yada karairayi game da jihar Xinjiang, har da shafa wa kamfanonin kasar Sin da ke gudanar da ayyuka a ketare kashin kaza, duka ba su rasa nasaba da kasar Amurka ba. Sai kuma a yayin da Sin da kasashen Afirka suka yi ta inganta hadin gwiwarsu, har kuma aka aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya” yadda ya kamata, tattalin arzikin kasashen da abin ya shafa ya yi ta bunkasa, kuma manyan ababen more rayuwa da ma rayuwar al’ummar kasashen ma sun kyautata. Amma Amurka wadda ta dade tana nuna fin karfi a duniya ba ta ji dadin hakan ba, don haka ma muke ta kara karanta rahotanni da ke shafar “sabon salon mulkin mallaka” da “tarkon bashi” da “barazana daga kasar Sin” a rahotannin da kafofin yada labarai na kasashen yamma suke watsawa.
A cewar Mista Jan Oberg, bai ga barazanar da kasar Sin ke haifarwa Amurka daga manufofin diplomasiyyarta ba, ya ce, kasar Sin ba ta tura jiragen ruwan sojanta zuwa bakin teku na California ko na Florida ba, a akasin haka kuma, kasashen yamma sun “kewaye” kasar Sin da jiragen ruwan sojansu.
Jama’a, ku yi hankali a lokacin da kuke karanta rahotannin da ke shafa wa kasar Sin bakin fenti, sabo da ta yiwu sun shafi shirin dokar nan ta dala biliyan 1.5. Ban da haka, za mu so mu shawarci Amurka da ta maida hankali wajen gudanar da ayyuka masu ma’ana da za su amfani kasashen Afirka da ma sauran kasashe masu tasowa, maimakon furta kalaman banza da karairayi, kana ta taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasashen.(Lubabatu)