Bikin baje kolin kayayyakin sayayya na kasa da kasa na kasar Sin ko (CICPE) karo na 4 dake gudana a lardin Hainan na kasar Sin, ya janyo hankalin kamfanonin kasashe da yankuna 71, wadanda ke baje kolin kayayyakinsu masu tambura fiye da 4000. Wadannan alkaluma sun nuna wani yanayi mai armashi da tattalin arzikin kasar Sin ke ciki. Za mu iya kara tantance yanayin tattalin arzikin Sin ta wasu bangarorin ayyuka guda 3.
Na farko, aikin sayayya. A rubi’in farko na bana, yawan darajar kayayyakin sayayya, da aka sayar da su a kasuwannin kasar, ya karu da kashi 4.7%. Kana a cikinsu, ayyukan hidimomin da aka sayar da su sun karu da kaso 10%. Ban da haka, gwamnatin kasar Sin tana sa kaimi ga aikin maye gurbin tsoffin kayayyakin gida da sabbi, wanda shi ma zai taimakawa raya bangaren sayayya a kasar sosai.
- Firaministan Sin: Tarihin Canton Fair Ya Nuna Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Fadada Bude Kofarta Ga Kasashen Waje
- Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Ya Gana Da Takwararsa Ta Afirka Ta Tsakiya
Na biyu shi ne amfani da sabbin fasahohi na samar da kayayyaki masu inganci. Wannan manufa tana inganta tsarin tattalin arzikin kasar, inda alkaluma na rubu’in farko na bana suka nuna cewa, saurin karuwar bangaren samar da ingantattun kayayyaki masu kunshe da fasahohin zamani, a cikin manyan masana’antun kasar Sin, ya karu da kashi 7.5%, idan an kwatanta da na bara.
Yayin da fanni na 3 zai shafi hasashen da ake yi, ganin yadda makomar tattalin arziki da ake sa ran samu take da matukar muhimmanci ga yanayin ci gaban tattalin arziki. Inda a wannan fanni ma, kasar Sin take da fifiko sosai, saboda mutane na kasashe daban daban sun gane ma idanunsu yadda tattalin arzikin Sin ya samu farfadowa sosai a rubu’in farko na shekarar da muke ciki. (Bello Wang)