Ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi a kasar Rasha tsakanin ranar 7 zuwa 10 ga watan Mayun da muke ciki, tare da halartar bikin tunawa da cika shekaru 80 da samun nasara a yakin kare kasa na tarayyar Soviet daga mahara, da ya gudana a birnin Moscow, sun nuna zumunta da huldar hadin kai masu karfi da aka samu tsakanin kasashen Sin da Rasha.
Yayin da duniyarmu ke fuskantar mummunan tasirin da ra’ayin kariyar ciniki, da rashin daidaito tsakanin kasashe daban-daban a fannin ci gaban tattalin arziki, suka haddasa, kasashen Sin da Rasha na kokarin samar da gudummowa ga yunkurin farfado da tattalin arzikin duniya a hadin gwiwarsu. A lokacin ziyarar shugaba Xi Jinping a kasar Rasha ta wannan karo, bangarorin Sin da Rasha sun kulla yarjeniyoyi fiye da 20, wadanda suka shafi fannonin zuba jari, da tattalin arziki mai nasaba da fasahohin zamani, da sana’ar daukar fina-finai, da dai makamantansu. Ban da haka, kasashen biyu sun tabbatar da niyyar ba da taimako ga karin kasashe masu tasowa, don su taka rawar gani a cinikayyar duniya.
Haka zalika, yayin ganawar shugabannin Sin da Rasha a wannan karo, sun tabbatar da karfafa hadin kan kasashen su, a Majalissar Dinkin Duniya, da kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO), gami da tsarin BRICS, inda za su yi kokarin kare tsarin ciniki na duniya mai kunshe da bangarori masu fada a ji daban daban, da tabbatar da gudanar tsare-tsaren samar da kayayyaki na duniya yadda ake bukata. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp