A yau Laraba ne kotun kolin Nijeriya za ta yanke hukunci kan matsayin kujerar gwamnan jihar, tsakanin Rt Hon Ahmadu Umaru Fintiri, rantsatstsen gwamna da Sanata Aishatu Ahmad Binani, da ke kalubalantar kujerar.
Idan za’a tunawa, a ranar Litinin ne kotun koli ta jingine hukuncin bayan kammala gabatar da sauraren korafe-korafe daga lauyoyin Aishatu da Fintiri.
Binani, ‘yar takarar gwamna karkashin jam’iyyar APC a zaben 2023, ta shigar da kara tana mai kalubalantar ayyana Ahmadu Umaru Fintiri, da hukumar zabe ta kasa, INEC ta yi a matsayin zababben gwamnan jihar Adamawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp