Cutar Hassada wata cuta ce ko ciwo da ke yawo ya kafa reshe da jijiya a cikin jinin dan’Adam, kuma wannan cuta magance ta abu ne mai matukar wahala, wanda sai mutum ya jajirce ya yi yaki da zuciyarsa tare da hadawa da addu’o’i.
Idan yanayin rayuwa ya zo maka da sauyi irin na cigaba ko na daukaka ko dai wani abu makamancin haka to tabbas ka shirya fuskantar kalubalen hassada wanda dole mutum sai ya jajirce wurin yi wa Ubangiji da’a, ibada sannan ka kasance mai matukar hakuri. Har sanda Allah zai so ka yi nasara akan masu yi maka hassada.
- Amfanin Aloe Vera A Jikin Mace
- Harin Bam A Kaduna: Sanatoci 109 Sun Bayar Da Gudummawar Albashinsu Naira Miliyan 109
Akwai karin magana da Bahaushe ya ke cewa hassada ga mai rabo taki ce, tabbas wannan batu haka yake. Kamar misali shuka ce a gona ta girma ta fito koriya shar sanadiyyar ingantaccen taki da kuma kula da ita samu to haka abin yake ga wanda ake yi wa hassada zai kasance mai samun ci gaba da daukaka a rayuwa a kowane lokaci
Akwai wasu misalai na wasu abubuwa da suka faru wanda mun gansu ko kuma mun ji su a tarihi wanda zahiri sun faru iri su Tarihin Annabi Yusuf Alaihissalam. Duk wani Musulmi ko a makarantu Islamiyya ko kuma a gidaje ko majalisu ya san tarihin Annabi Yusuf, wanda ‘yan uwansa suka tsane shi tare da yi masa hassada har ta kai ga sun yi yunkurin kashe shi.
Cikin ikon Allah shi da suke wa hassada sai da ya sami daukakar da basu taba tsammani ba. Shi ne karaminsu amma kuma sai da rayuwa ta juya suka dawo karkashinsa, suka fahimci cewar ga yarima ya sha gabansu.
A wurin aiki za ka ga nan ma ana yawan fuskantar kalubale na hassada wanda za ka ga abokan aiki na bakin ciki da samun da ko kuma daukar da ka fi su a wurin, in ya hadu da imaninsu akwai rauni sai ka ga ana neman hallaka rayuwar mutum.
Haka a cikin ‘yan uwa ma wannan matsala tana tasiri sosai har ka ga gaba ko rashin jituwa na shiga tsakani.
Saboda haka ma’aurata suma a wannan fannin ya kamata su yi kokarin kame zuciyoyinsu domin kuwa shaidan na iya rinjayar zamantakewarsu har ta kai ga hassada ta shiga lamarin zamansu ko kuma ‘yan uwansu.